Barcelona ta ce gwaji ya nuna Sergi Roberto ya harbu da cutar COVID-19

Barcelona ta ce gwaji ya nuna Sergi Roberto ya harbu da cutar COVID-19

-Gwajin da aka yi ranar Talata ya nuna Sergi Roberto ya kamu da COVID-19

-‘Dan wasan da yanzu yake fama da rauni a cinya, zai ji da jinyar Coronavirus

-Kungiyar Barcelona na cikin matsalar karancin ‘yan wasa sakamakon rauni

Bayan an yi gwaji a ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba, 2020, an gano cewa ‘dan wasan Barcelona, Sergi Roberto yana dauke da kwayar cutar COVID-19.

Kungiyar Barcelona ta bada wannan sanarwa a shafinta na yanar gizo a ranar Laraba da safe.

Barcelona ta bayyana cewa ‘dan wasan garau yake, har yanzu cutar ba ta kwantar da shi ba. Sai dai ya killace kansa a gida domin takaita yaduwar cutar.

Hakan na zuwa ne bayan ‘dan wasan ya kwanta jinya a sakamakon raunin da ya samu a ranar 21 ga watan jiya, bayan nan kuma ya harbu da Coronavirus.

KU KARANTA: An fara gano abin da ya yi sanadiyyar mutuwar Maradona

A wasan Atlético Madrid da Barcelona ne ‘dan wasan ya ji ciwo a cinya. Tauraron zai shafe watanni akalla biyu yana jinya, ba tare da ya taka leda ba.

Kamar yadda jawabin da Barcelona ta fitar dazu ya bayyana, an sanar da ma’aikatan lafiya da sauran hukumomin da su ka dace game da wannan lamari.

Malaman asibiti sun yi amfani da gwajin PCR wajen bibiyan duk wadanda suka samu wata alaka da ‘dan wasan bayan da nufin a dakile yada wannan ciwo.

Jaridar AS ta Sifen ta ce tun bayan da Samuel Umtiti ya kamu da Coronavirus a watan Agusta, a duk mako sai an yi wa ‘yan wasan Barcelona gwaji sau biyu.

KU KARANTA: Shugaban kungiyar Barcelona ya yi murabus

Barcelona ta ce gwaji ya nuna Sergi Roberto ya harbu da cutar COVID-19
Sergio Roberto Hoto: goal.com
Asali: UGC

‘Dan wasan na Sifen shi ne na uku da cutar ta harba a cikin manyan ‘yan wasan kungiyar. Sabon ‘dan wasan tsakiya, Miralem Pjanic, ya yi jinyar cutar kwanaki.

A watan Oktoba kun ji cewa babban 'Dan wasan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo ya shiga sahun wadanda su ka kamu da cutar murar mashako ta COVID-19.

Hukumar kwallon kafa na kasar Portugal ta fitar da jawabi a lokacin da ake buga wasannin kasa da kasa. Tuni Dan wasan mai shekaru 35 ya samu lafiya a gida.

A wancan lokaci an zargi ‘dan wasan da saba dokoki da sharudan da malaman lafiya su ka sa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel