Yanzu-yanzu: Bartomeu ya yi murabus a matsayin shugaban Barcelona

Yanzu-yanzu: Bartomeu ya yi murabus a matsayin shugaban Barcelona

- Joseph Bartomeu ya bata wa kansa suna bayan rikicin da ya yi da Lionel Messi a watannin da suka gabata

- Tauraron na Barcelona Lionel Messi da farko ya mika wa kungiyar wasikar neman tafiya amma daga bisani ya canja ra'ayinsa

- Shugaban kungiyar Josep Bartomeu ya yi murabus tun kafin ayi masa kuri'ar rashin amincewa a kore shi

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Maria Bartomeu ya yi murabus a ranar Talata 27 ga watan Oktoba kafin a jefa kuri'ar rashin amincewa a kansa kafin a kore shi kamar yadda SunSport ta ruwaito.

An kuma gano cewa wasu direktocin kungiyarda dama suma sun yi murabus daga matsayinsu.

Yanzu-yanzu: Bartomeu ya yi murabus a matsayin shugaban Barcelona
Yanzu-yanzu: Bartomeu ya yi murabus a matsayin shugaban Barcelona. Hoto: Noelia Deniz
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Abinda yasa ba mu janye yajin aiki ba - ASUU

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan kungiyar ta Barcelona ta sha kaye 3-1 a hannun abokan hammayarsu na gida Real Madrid a El Classico ta farko na wannan kakan wasar.

Sunan Bartomeu ta baci ne bayan yadda ta kaya tsakaninsa da fitaccen dan wasan kungiyar Lionel Messi wadda da farko ya mika wasikarsa ta neman barin kungiyar.

Ya ki canja ra'ayinsa wadda hakan ya kusa saka fitaccen dan wasan da ya lashe Ballpn d'Or guda shida barin kungiyar bayan shekaru 20.

Magoya bayan kungiyar wadda sune suka mallaki kungiyar sun yi taro sun kuma samu adadin sa hannu da ake bukata don fara yi jefa masa kuri'an rashin amincewa.

KU KARANTA: Mutum 5 sun mutu yayin rabon kuɗin da suka tsinnta a ma'ajiyar kayan tallafin korona

Idan ba a manta ba tunda farko da Messi ya yi barazanar barin kungiyar, mahaifinsa Jorge ya shiga jirgi ya zo Barcelona amma ba su daidaita ba.

Kuma duk da kullen korona da aka saka a kasar, magoya bayan kungiyar sun yi tururuwa zuwa Camp Nou inda suka bukaci Bartomeu ya yi murabus.

Hakan ne ya janyo suka fara shirin tattara kuri'u don jefa zaben rashin amincewa da shi.

An zargi Bartomeu da rashawa a watan Satumba yanzu ya yanke shawarar yin murabus kafin a kore shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164