COVID-19: Gwaji ya tabbatar da Cristiano Ronaldo ya na dauke da cuta
- An tabbatar da cewa Cristiano Ronaldo ya kamu da cutar Coronavirus
- ‘Dan kwallon ba zai samu damar buga wasan Portugal da Sweden ba
- Hukumar kwallon kafa na kasar Portugal ta fitar da jawabi dazu nan
‘Dan wasan kwallon kafa Cristiano Ronaldo ya shiga sahun wadanda su ka kamu da cutar murar mashako ta COVID-19.
A yau Talata, 13 ga watan Oktoba, 2020, aka tabbatar da cewa Cristiano Ronaldo ya na dauke da kwayar cutar Coronavirus.
Hukumar kwallon kafa na kasar Portugal ta shaidawa Duniya wannan a yau da rana.
Hukumar kwallon kafa na Portigal ta fitar da jawabi:
KU KARANTA: 'Dan wasan Liverpool ya kamu da COVID-19
“A sakamakon bullar cutar da aka samu, an yi wa sauran ‘yan wasa gwaji a yau Talata da safe, dukkansu ba su dauke da cutar.”
Cidade do Futebol ta tabbatar da cewa a shirye sauran ‘yan kwallon su ke da su bugawa Koci Fernando Santos.
A dalilin wannan, ‘dan wasan gaban ba zai samu damar buga wasan Portugal da kasar Sweden wanda za ayi gobe ba.
Sky Sports News ta rahoto cewa alamun wannan cuta ba ta fara bayyana a kan ‘dan wasan na Juventus mai shekara 35 ba.
KU KARANTA: Taurarin Super Eagles za su yi jinyar Coronavirus
Rahotanni sun bayyana cewa ‘dan wasan ya na nan garau, amma ya killace kansa daga jama’a.
A ranar Laraba ne kasar Portugal za ta kara da Sweden a garin Alvalade a gasan cin kofin kasashen Nahiyar Turai da ake yi.
A watan Satumba kun ji yadda ‘Dan wasan gaban kungiyar AC Milan Zlatan Ibrahimovich ya kamu da cutar Coronavirus.
An tabbatar da haka a ranar 24 ga watan Satumba. Bayan 'yan kwanaki, 'dan wasan ya warke.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng