Harin Zabarmari: Buhari ya nemi Dakarun Sojoji su shiga inda Boko Haram suke

Harin Zabarmari: Buhari ya nemi Dakarun Sojoji su shiga inda Boko Haram suke

-Muhammadu Buhari ya tura tawagar ta musamman ta je kauyen Zabarmari

-Wannan tawaga ta isa Borno jiya, kuma ta ba al’umma sakon shugaban kasa

-Shugaban Najeriya ya umarci sojoji su tashi, su shiga duk inda Miyagu suke

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba dakarun sojojin Najeriya umarni su kai yaki da ta’addanci har zuwa gaban ‘yan Boko Haram.

Jaridar Daily Trust ta ce shugaban kasar ya nemi jami’an tsaro su shiga duk inda ‘yan ta’addan Boko Haram suke, har sai sun ga bayansu kaf.

Mai girma shugaban kasa ya sanar da wannan umarni ne a sakon da aka aika a madadinsa lokacin da tawagar da ya tura ta isa Zabarmari.

Tawagar shugaban kasar wanda Ahmed Lawan da Ibrahim Gambari suka jagoranta sun yi wa mutanen jihar Borno magana da yawun Buhari.

KU KARANTA: A gano gawa fiye da 30 sun fara kumbura a Zabarmari

Muhammadu Buhari ya yi alkawarin hada-kai da makwabta da sauran kasashen Duniya domin tabbatar da cewa Boko Haram ta rasa mafaka.

Shugaban kasar ya kuma sha alwashin ware dukiya mai tsoka domin ganin sojoji sun samu nasara. Jaridar Daily Trust ta rahoto wannan a jiya.

Buhari ya ke cewa: “Babu abin da ya fi kare rai da dukiyoyin jama’a muhimmanci. Komai zai zo daga baya ne muddin ba a samu wanzuwar tsaro ba.”

“Yayin da muke makokin ‘ya ‘yanmu a Zabarmari, an ba sojojin kasa umarni su cigaba da kutsa wa inda masu tada kayar baya suke.” Inji Buhari.

KU KARANTA: Abin da ya kamata Buhari ya yi - Zulum

Shugaban na Najeriya ya ce abin ba zai zama yau ayi-gobe a tsaya ba, ya ce za a cigaba da kokarin ganin an tsefe ‘yan ta’addan daga duk inda suke fake.

A ranar Litinin shugaban kasa ya tada tawaga ta musamman mai kunshe da Hadimai, Ministoci da ‘Yan majalisa domin suyi wa al’ummar Borno ta’aziyya.

Idan za ku tuna sauran ‘yan tawagar sun had da Hon. Tahir Monguno, Muhammed Musa Bello, Dr. Isa Ali Pantami, Mustapha Shehuri, da kuma Abubakar Aliyu.

Ragowar su ne: Mai bada shawara a kan harkar tsaro, Janar Babagana Monguno da Garba Shehu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel