Shugaban Hafsun Soji, Janar Buratai ya maida raddi a kan kalaman Magauta
- Shugaban sojojin kasa ya yi magana game da kiran da ake yi na tsige shi
- Laftana Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce wasu sun jahilci aikin gidan soja
- Buratai ya ce za a iya kara wasu shekaru ba a ga karshen Boko Haram ba
Shugaban sojojin kasan Najeriya, Laftana Janar Tukur Buratai, ya yi wa masu sukar manyan jami’an tsaron kasar nan raddi a kan halin rashin tsaro.
Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi magana ne bayan an huro wuta a kan cewa ya kamata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya canza hafsun tsaron kasar.
Jaridar Daily Nigerian ta rahoto cewa Tukur Yusuf Buratai ya yi wannan magana ne a shafinsa na Facebook, ya na nuna cewa yanzu aka fara yaki da miyagu.
Wasu da-dama suna ganin bai dace Tukur Buratai da takwarorinsa su cigaba da zama a ofis har yanzu ba.
KU KARANTA: Wadanda aka yi wa kisan gilla ba su nemi iznin zuwa gona ba ne
A shafinsa na Facebook, babban sojan ya ke cewa fadan da ake yi da ‘yan ta’adda da masu tada zaune-tsaye, zai iya kai akalla wasu shekaru 20 masu zuwa.
“Jama’a sun yi tarayya wajen rashin fahimtar abin da yakin sunkuru da ta’addanci ya kunsa. Akwai yiwuwar a kara shekaru 20 ana fama da ta’addanci.”
Buratai ya ce: “Ya danganta ne da yadda abin ya rincabe da kuma martanin da duk wasu masu ruwa da tsaki suke yi; jami'an sojoji da kuma masu farar hula.”
Hafsun sojan kasar ya ce dole mutanen gida da na kasar waje su bada gudumuwarsu a yankin.
KU KARANTA: Gwamnonin Jihohi za su zauna da nufin a kawo karshen matsalar tsaro
“Akwai matukar bukata da tasirin al’umma. Dole duk su hada kai wajen shawo kan sha’anin rashin tsaron da ya ki ci, ya ki cinyewa.” Inji Janar Tukur Buratai.
Daily Nigerian ta rahoto hafsun sojin kasar ya na kira a tashi tsaye, a kawo karshen matsalar.
Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana dalilin da yasa Muhammadu Buhari ya ke ci gaba da barin shugabannin tsaro a ofis.
Garba Shehu ya ce nada shugabannin tsaro ko tsige su ikon shugaban kasa ne, kuma yana da damar ci gaba da barinsu idan har ya gamsu da kokarin da su ke yi.
Hadimin shugaban kasar ya soki kiran da wasu su ke yi na ganin an canza hafsoshin tsaron.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng