Rundunar soji ta bayyana wadanda ke wa tsaro zagon kasa a arewacin Najeriya

Rundunar soji ta bayyana wadanda ke wa tsaro zagon kasa a arewacin Najeriya

- A ranar Litinin, rundunar sojin Najeriya sun yi korafi a kan yadda mazauna Maiduguri suke boye musu bayanai a kan 'yan ta'adda

- A cewar Kakakin rundunar sojin, akwai labarai da ya kamata mazauna yankunan su din ga sanar dasu don su yi bincike a kansu

- Ya ce ya ji labarin UN tace mutane 110 ne aka kashe, amma sojoji da 'yan kauyen Zabarmari sun kirga gawawwaki 43

A ranar Litinin, rundunar sojin Najeriya ta nuna takaicin yadda wasu 'yan arewa maso gabas suke kin bai wa jami'an tsaro bayanai wadanda za su taimaka wurin bincike.

A kalla manoma 43 ake zargin 'yan Boko Haram sun kashe a Zabarmari, jihar Borno a ranar Asabar, Channels TV ta ruwaito.

UN ta ce kisan da aka yi ya kai mutane 110. Sannan wannan harin da aka kai na kwanan nan ya yi tsanani a cikin hare-haren arewa maso gabas da ake kaiwa.

KU KARANTA: Hotunan Sarakuna 6 na Najeriya masu karancin shekaru da tsabar ado

Rundunar soji ta bayyana wadanda ke wa tsaro zagon kasa a arewacin Najeriya
Rundunar soji ta bayyana wadanda ke wa tsaro zagon kasa a arewacin Najeriya. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

Amma kakakin rundunar sojin, manjo janar John Enenche, ya bayyana a gidan talabijin na Channels inda yace abubuwan da ke kawo tabarbarewar tsaro har da yadda mazauna yankuna suke kin bayar da bayanai wadanda za su taimaki sojoji.

"Wannan shine damuwarmu. Yana matukar damun mu, muna bukatar bayanai, su ne mazauna yankunan, idan sun ga wata matsala ta barke, yakamata su sanar da mu," yace.

Ya ce idan sun tafi sintiri, lokacin da zasu dawo sai suga IED a hanyoyi, kuma mutanen yankunan suna sane da 'yan ta'addan, amma sai suki fadi musu. Wannan ita ce babbar matsalar da suke fuskanta.

"Kuma ba zai yuwu mu matsa musu don su sanar damu matsalar ba."

A cewarsa, sojoji ne suka raka gwamna Zulum zuwa inda aka kashe mutane 43 din.

Sannan yace yaji labarin UN suna cewa mutane 110 ne aka kashe, amma su dai sojoji sun kirga gawawwaki 43 tare da mazauna kauyen, kuma a kan haka za su zauna.

Amma za su cigaba da bincike don tabbatar da asalin yawan mutanen.

KU KARANTA: Tashan wutan lantarki ta kasa ta lalace, sunayen jihohin da rashin wuta zai shafa

A wani labari na daban, a ranar Asabar, sojojin Najeriya sun samu nasarar ragargazar maboyar 'yan Boko Haram da dama.

Kamar yadda wata takarda wacce kakakin rundunar 'yan sojin, John Enenche ya sa hannu, rundunar sojin sama sun yi wata ragargaza a ranar Juma'a, inda sabuwar rundunar da aka kirkira karkashin Operation Lafiya Dole, mai suna 'Wutar Kabir II' ta aiwatar da harin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel