Gwamna jihar Yobe kwana uku yake a jiharsa, daga Abuja yake mulki

Gwamna jihar Yobe kwana uku yake a jiharsa, daga Abuja yake mulki

- Gwamnan Buni yana rike manyan mukamai biyu a jiharsa da birnin tarayya

- Yayinda ofishinsa na gwamna ke jihar Yobe, na shugabancin jam'iyya na Abuja

- Ya bayyana yadda yake raba zaman da yakeyi tsakanin Abuja da Yobe

Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar All Progressives Congress APC, Mai Mala Buni, ya ce yana kwana uku a wata a jiharsa.

A hirar da yayi da BBC, gwamnan yace yana mulkan al'ummarsa kwarai da gaske duk da cewa ba ya zama a jihar.

Buni ya bayyana hakan ne yayin martani kan sukar da ake masa cewa ba ya zama a jihar tun lokacin da ya zama shugaban rikon kwaryan jam'iyyar APC.

Ya kara da cewa aikinsa na shugabancin jam'iyyar ba ya hanashi aiwatar da ayyukansa na gwamna.

"Akan lamarin zama, ba zai yiwu a yi wata daya ban kwashe kwana uku ko hudu a jihar Yobe ba. Kuma ko da na koma Yobe, ba na shela cewa yau zan koma ko gobe zan tafi," gwamnan yace.

"Zamanin fasaha da muke ciki, ta yaya wani zai ce akwai tarin takardun aiki suna jira na? Ko kafin inzo (hirar) nan, ban san adadin takardun da na duba ba."

KU KARANTA: Kada ka cire takunkumin hana shigo da shinkafa, gwamnan Benue ya bukaci Buhari

Gwamna jihar Yobe kwana uku yake a jiharsa, daga Abuja yake mulki
Gwamna jihar Yobe kwana uku yake a jiharsa, daga Abuja yake mulki Hoto: Presidency
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kisan Borno: Lokacin sauya tsarin tsaro yayi, Lawan ga Gwamnatin tarayya

A wani labarin, kwamitin kula da tsare-tsare na jam'iyya mai mulki, APC, sun ce sun kammala duk shirye-shirye don fara aiwatar da sabuwar rijista da sabunta rijistar ƴan jam'iyya daga ranar 12 ga watan Disamba.

Shugaban kwamitin, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ne ya fadi hakan a sanarwar da suka fitar a birnin tarayya, Abuja, ranar Litinin bayan ganawa da masu ruwa da tsaki, wanda suka haɗa da Shugaba Muhammad Buhari.

Ya ce za'a fara rijistar shaidar zama ɗan jam'iyya daga ranar Asabar, 12 ga Disamba, 2020 zuwa Asabar, 9 ga watan Junairu, 2021.

"Mu na gayyatar dukkan ƴan jam'iyyarmu da su sabunta shaidarsu a mazaɓunsu." Yace

"Haka zalika muna kira da ƴan jam'iyya da basu da rijista da suyi amfani da wannan damar don zama cikakkun ƴan jam'iyyarmu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng