Boko Haram ta taba zaben kwamishina a Borno, dan jarida ya tona asirin tushen ta'addanci

Boko Haram ta taba zaben kwamishina a Borno, dan jarida ya tona asirin tushen ta'addanci

- Wani dan jaridan Najeriya, David Hundeyin ya fallasa sabubban Boko Haram a Najeriya

- A cewarsa, tun bayan ya kammala bincike ya daina tausayin wadanda 'yan Boko Haram suke cutarwa

- A cewarsa, 'yan siyasan arewa, irin su Yerima sune suka bata tunanin matasan Boko Haram

Wani dan jarida dan Najeriya, David Hundeyin ya bayyana yadda aka kirkiri Boko Haram a Najeriya, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Hundeyin ya zargi arewa da kirkirar muguwar kungiyar da yanzu ta girma ta fi karfin gwamnati, ya ce ya daina tausayawa wadanda ta'addancin ya shafa tun bayan ya yi bincike a kan yadda aka kirkiri kungiyar a arewa a 2019.

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter;

Lokacin da nayi rahotonni a kan asalin kungiyar a arewa shekarar da ta gabata, sai na daina tausayawa gabadaya.

Dakansu suka kirkiri azzalumar kungiyar wacce yanzu haka tayi karfin da kyar a iya rusheta. Ina so in fallasa wani abu a wannan wallafar tawa, wacce baku taba sani ba.

KU KARANTA: Turmi da tabarya: Matashi mai shekaru 19 ya mutu a kan karuwa a Legas

Boko Haram ta taba zaben kwamishina a Borno, dan jarida ya tona asirin tushen ta'addanci
Boko Haram ta taba zaben kwamishina a Borno, dan jarida ya tona asirin tushen ta'addanci. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

Ko kun san cewa shugabannin siyasa masu amfani da shari'a a arewacin Najeriya sun dade suna ce musu duk wuraren da kiristocin arewacin Najeriya suke zaune tun asalin mallakin musulmai ne a ka'idar shari'ar musulunci? Bari in yi muku bayani.

Saboda tsarin auren mace guda daya da kiristoci suke da su, yawan yaran da za su nemi gadon iyayensu na wurare basu da yawa, wanda hakan yake basu dama a wuraren da filaye ne mafificin dukiya.

Musulman arewa kuma saboda yawan auren mata, filayen da ake basu a matsayin gado basu isarsu. Misali mutum mai yara 17, 8 cikinsu maza ne, filayen da aka basu, sun yi musu kadan.

Shiyasa shugabannin siyasa na arewa irin su Yerima suka yi amfani da damar wurin cewa mabiyansu, filayen "arna" nasu ne.

Ustaz Mohammad Yusuf, mai wa'azin nan mai dadin baki ya yi amfani da damar nan yayi ta raina wa mabiyansa wayau yana ce musu duk yankin arewa nasu ne.

A 2007, Boko Haram har zabar kwamishina suka yi a jihar Borno. Al'amarin ya lalace ne bayan Gwamna Ali Modu Sheriff ya ki bin dokokin da Boko Haram suka gindaya masa, ciki kuwa har da kwatar filayen arna don ya rabawa matasa musulmai.

Yusuf ya ballo rikici kuma 'yan sanda a watan Yulin 2009 sun yi yadda suka saba, wato kisa ba tare da alkali ya bayar da umarni ba a babban ofishin 'yan sanda dake Maiduguri. Daga nan mataimakinsa, Abubakar Shekau ya cigaba daga inda ya tsaya, har ta kai yau.

KU KARANTA: Kisan Manoma 40: Ka sauya tsarin tsaron kasa, Atiku ga Buhari

A wani labari na daban, a ranar Asabar, sojojin Najeriya sun samu nasarar ragargazar maboyar 'yan Boko Haram da dama.

Kamar yadda wata takarda wacce kakakin rundunar 'yan sojin, John Enenche ya sa hannu, rundunar sojin sama sun yi wata ragargaza a ranar Juma'a, inda sabuwar rundunar da aka kirkira karkashin Operation Lafiya Dole, mai suna 'Wutar Kabir II' ta aiwatar da harin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel