2023: Fashola ya bayyana abinda ya dace APC tayi domin cigaba da mulki

2023: Fashola ya bayyana abinda ya dace APC tayi domin cigaba da mulki

- Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya ce APC za ta cigaba da mulki a 2023, matsawar sun cika alkawuransu

- Ya ce wajibi ne 'yan siyasa su dage wurin cika alkawuran da suka daukar wa al'umma don hakan ne abinda ya kamata

- A cewarsa, nasara tana harararsu, saboda gwamnonin jihohin da a baya suke adawa da su, yanzu sun fara komawa APC

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya ce jam'iyyar APC za ta cigaba da mulki a 2023, matsawar ta cika wa 'yan Najeriya alkawuran da ta daukar musu.

Fashola ya fadi hakan a wata zantawa da manema labarai suka yi da shi a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba a Abuja.

A cewar tsohon gwamnan jihar Legas din, 'yan kasa za su zabi jam'iyyar da ta cika musu alkawuran da ta dauka, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

"Wasu daga cikin gwamnonin jihohin da muke tunanin mutane ba za su zabemu ba sun fara dawowa jam'iyyarmu.

2023: Fashola ya bayyana abinda ya dace APC tayi domin cigaba da mulki
2023: Fashola ya bayyana abinda ya dace APC tayi domin cigaba da mulki. Hoto daga @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

KU KARANTA: Cunkoso: Bata-gari sun kai wa kwamitin fadar shugaban kasa hari a Legas

"Don rike kujerunmu a 2023, wajibi ne mu cika alkawuran da muka daukar wa mutane, don su kara zabar mu.

"Hakan shine gaskiya, ba wai siyasa ba. Idan mutum yace zai yi, ko da bai yi dari bisa dari ba, a kalla idan aka ga yana kokari, za a yarda da cewa ka fara ayyuka,.

"Ya kamata a ce jam'iyyar da ke adawa damu, ta fi mu irin wannan tunanin don cin nasara a kanmu. Yanzu haka ba su yin irin wannan tunanin, kuma ba zan koya musu yadda za su yi ba," a cewarsa.

KU KARANTA: Da duminsa: Masu hidmar kasa 138 sun harbu da cutar korona

A wani labari na daban, hankula sun karkata a kan jam'iyyar APC ta jihar Legas a kan zaben 2023, da kuma hanyoyin dakatar da shugaban jam'iyyar, Asiwaju Bola Tinubu.

Duk da dai har yanzu zaben 2023 yana da tazara, jam'iyyar APC ta jihar ta shiga tararrabi a kan yadda masu fadi a ji suka fara nuna kwadayin mulkin jihar Legas, karara.

Ba nuna kwadayin mulkin kawai suka fara ba, suna ta nuna cewa Tinubu bai isa ya dakatar da su ba, duk da matsayinsa na shugaban jam'iyyar a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel