Kaduna: An shafe dare guda ana musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan bindiga a Jaji

Kaduna: An shafe dare guda ana musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan bindiga a Jaji

- Rahotanni sun bayyana cewa an shafe tsawon dare ana barin wuta a tsakanin sojoji da 'yan bindiga a tsakanin Zaria zuwa Kaduna

- 'Yan bindiga sun matsa wajen yawaita kai hare-hare a yankin Zaria da kewaye a 'yan kwanakin baya bayan nan

An shafe tsawon dare guda ana gumurzu tsakani jami'an sojoji da ƴan bindiga akan titin Zaria zuwa Kaduna.

Mun samu rahotannin cewa an shafe daren ranar Lahadi zuwa wayewar garin ranar Litinin ana ta faman bata kashi tsakanin sojoji da ƴan ta'adda daga titin Zariya zuwa Kaduna daf da garin Jaji, a cewar BBC Hausa.

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, shine ya tabbatarwa da BBC afkuwar lamarin yayin wata ganawa, inda ya bayyana cewa al'amarin ya faru a kusa da garin Jaji.

Ya ce sun tura jami'an tsaron don daƙile maharan daga aikita ta'addanci bayan sun sami rahotannin sun kai hari.

KARANTA: Bidiyo: Sheikh Daurawa ya bayyana ake wulakanta Malamai idan sun je ganin shugaban kasa domin yi masa nasiha

Wani maƙwabcin yankin ya ce tun a daren Lahadi, ƴan fashin suka tare hanyar tsakanin Jaji da kwanar Faraƙwai, kana suka tare hanyar da ke tsakanin Lamban Zango da Dumbi-Dutse.

Kaduna: An shafe dare guda ana musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan bindiga a Jaji
Kaduna: An shafe dare guda ana musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan bindiga a Jaji @Daily_trust
Source: Twitter

Kwamishinan tsaron bai bayar da gamsassun muhimman bayanai dangane da ba-ta-kashin da aka yi.

Al'ummar yankin sun shaidawa BBC cewa ƴan bindigar sun kashe mutane biyu a wata motar alfarma ƙirar Luxurious, sannan jami'an tsaro sun sheƙe biyu daga cikin ƴan bindigar.

Kana ɓarayin sun jikkata mutane da dama baya ga ƙwamushe wasu da yin garkuwa da su.

Sai dai wasu majiyoyi na cewa jami'an tsaro sun yi nasarar kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwar da su.

Jihar Kaduna dai na ɗaya daga cikin jihohin da ƴan bindiga daɗi ke cin karensu babu babbaka.

KARANTA: Rubdugun martani: Garba Shehu ya yi laushi, ya ce ba'a fahimci kalamansa da kyau ba a kan kisan manoma

Aƙalla mutane 16 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar ƴan bindigar a makonnin da suka gabata a yankunan jihar da suka haɗa da Zangon Kataf, Giwa da kuma Igabi.

Ƴan bindigar sun kai farmaki Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya inda suka sace Malamai da ƙananan yara, kana suka gangara jami'ar Ahmadu Bello suka sace wani Malami da iyalansa duk dai cikin makon da ya gabata.

Haka zalika, a cikin wannan makon ƴan ɓindigar sun kashe mutane huɗu a hanyar Kaduna Zuwa Abuja, daf da shiga ƙwaryar birnin jihar, a kusa da garin Kakau, Kaduna.

A baya Legit.ng ta wallafa rahoton cewa tsohon dan majalisa a Jamhuriya ta biyu, Dattijo Dakta Mohammed Junaid, ya ce ba za'a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba matukar shugaba Buhari da APC suna kan mulki.

A cewarsa, batun gyaran Najeriya fa ya fi karfin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Dakta Junaid ya bayyana hakan ne yayin da yake martani a kan kisan manoma 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a ranar Asabar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel