Sheikh Daurawa ya bayyana yadda makusanta Buhari ke wulakanta Malamai tare da hanasu ganinsa

Sheikh Daurawa ya bayyana yadda makusanta Buhari ke wulakanta Malamai tare da hanasu ganinsa

- 'Yan Nigeria na yawan tafka muhawara a kan cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, bai san halin da jama'a ke ciki ba a kasa

- Wasu na ganin cewa Malamai basa kokarin ganawa da shugabanni domin yi musu wa'azi, su fada musu gaskiya

- Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi bayani a kan yadda ganin shugaba Buhari ya gagari Malaman da suke ganinsa a baya

A yayin da 'yan Najeriya ke cigaba da muhawarar cewa ana rufewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari gaskiyar al'amuran da ke faruwa a kasa, wani faifan bidiyo na Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya zama ma'auni.

Daurawa, a cikin faifan bidiyon, ya bayyana cewa; "Wannan ƙasa tamu Najeriya Allah ka zaunar da ita lafiya,Allah muna cikin wani mayuwacin hali ba wanda zai fidda mu sai kai, Allah ka fidda mu.

"Shuwagabannimu Allah ka cika zukatansu da tausayi da jinƙai,ka cika zukatansu da rahama, ka haɗasu da mashawarta na ƙwarai.

Sheikh Daurawa ya bayyana yadda makusanta Buhari ke wulakanta Malamai tare da hanasu ganinsa
Sheikh Daurawa ya bayyana yadda makusanta Buhari ke wulakanta Malamai tare da hanasu ganinsa
Asali: UGC

"Wallahi har tausayin mutum nake ace ya zama shugaba a Najeriya saboda mugaye da miyagun mashawarta.

KARANTA: 'Yan ta'adda sun tashi sinadarai masu fashewa a Cocin mahaifin gwamna Wike

"Wallahi ka zama shugaba ko na ƙaramar hukuma, ko na jiha, ko na ƙasa, makaho ake maida kai, bebe ake maida kai, kurma ake maida mutum, Wallahi ba za'a yarda ka ɗau komai ba,ba za'a yarda ka ji komai ba,kuma ba za'a yarda kasan komai ba.

"Sai kaga lokacin da kake jawabi kana ƙarya, mutanen ƙasa kuma sun san ba haka bane saboda wanda suka rubuta maka, shirme suka rubuta maka, sun ci amana.

KARANTA: An cire kwamandan bataliyar sojojin da ke Zabarmari bayan kisan manoma 43

"Mafi yawan wadanda suke kewaye da shugabanni wallahi ba masu ƙaunar ƙasa da alheri bane.

"Idan ka zo za ka ga shugaban ƙasa an ringa yi maka wuru-wuru kenan har sai an koreka. Duk zuwan da muke yi domin mu bada shawara sai da akayi wuru-wurun da aka hana mu zuwa. Ko kuma ace me zaka faɗa, Sai na ce kamar ya me zan faɗa?, nasiha zan yi.

"Wallahi da duk bayan wata uku sai an kwashemu mun je mun gana da shugaban ƙasa, amma yanzu Wallahi kusan shekara ɗaya da rabi kenan an hana mu zuwa."

Dangane da batun kisan manoma 43 a Jihar Borno, Legit.ng Hausa ta rawaito cewa ministan sadarwa, Dakta Isa Pantami, ya dauki alkawarin isar da sakon 'yan arewa ga shugaba Buhari.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng