Najeriya ta fi karfin Buhari, ba zai iya ba; Kalaman Dattijo Dakta Junaid

Najeriya ta fi karfin Buhari, ba zai iya ba; Kalaman Dattijo Dakta Junaid

- Batun kisan manoma 43, da mayakan kungiyar Boko Haram suka yanka, ya tayar da hankulan jama'a

- Jama'a da dama, musamman 'yan arewa, sun mamaye dandalin sada zumunta da alhinin kisan manoman

- Dattijo Dakta Mohammed Junaid, ya ce ba za'a taba samun zaman lafiya a Najeriya matukar APC da Buhari su na kan mulki

Tsohon dan majalisa a Jamhuriya ta biyu, Dattijo Dakta Mohammed Junaid, ya ce ba za'a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba matukar shugaba Buhari da APC suna kan mulki.

A cewarsa, batun gyaran Najeriya fa ya fi karfin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Dakta Junaid ya bayyana hakan ne yayin da yake martani a kan kisan manoma 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a ranar Asabar.

"Na san ya zuwa yanzu 'yan Najeriya sun gaji da labaran kisan fararen hula a yankin arewa maso gabas, musamman a jihar Borno.

KARANTA: Korafi: Pantami ya dauki alkawarin isar da sakon 'yan arewa ga Buhari

"Yanzu kuma babu sauran dan Najeriya da bai yarda cewa akwai 'yan bindiga da ke kashe mutane a arewa maso yamma, musamman jihar Zamfara, Katsina, Sokoto, da Kaduna ba.

Najeriya ta fi karfin Buhari, ba zai iya ba; Kalaman Dattijo Dakta Junaid
Najeriya ta fi karfin Buhari, ba zai iya ba; Kalaman Dattijo Dakta Junaid
Asali: Facebook

"To babu amfani a wurin wannan lusarar gwamnati ta ke aika sakon jaje duk lokacin da 'yan ta'adda suka kashe mutane, ya kamata a ce an wuce wurin da zasu ke fitowa suna cewa kisan fararen hula ya girgizasu.

"Duk abin da ya ke faruwa, ya na faruwa ne saboda babu gwamnati a kasar nan.

KARANTA: Da duminsa: An cire kwamandan bataliyar sojojin da ke Zabarmari bayan kisan manoma 43

"Matukar dai Buhari da APC za su cigaba da zama a gwamnati, ba za'a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba, mulkin Najeriya ya fi karfinsa, ba zai iya ba.

"Ya fadi kasa warwas, amma saboda munafurci irin na 'yan Najeriya, da kabilanci, da nuna bangaranci, da siyasar addini, wasu gani suke Buhari ya na tabuka wani kirki.

"Bai tabuka komai ba Kuma babu abinda zai iya yi, idan 'yan Najeriya suna son ganin canji sai su yi wani abu ko kuma su yi shiru, su daina korafi," a cewar Dakta Junaid.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa fashewar wasu sinadarai da ake ke zargin bama-bamai ne a Cocin mahaifin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya girgiza jama'a a wani bangare na birnin Fatakwal.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng