Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun yiwa manoma sama 40 yankan rago a jihar Borno

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun yiwa manoma sama 40 yankan rago a jihar Borno

Rahoton Premium Times na nuna cewa wasu da kae zargin yan Boko Haram ne su hallaka manoman shinkafa 44 a jihar Borno.

A cewar rahoton, sun hallaka manoman ne yayinda suke girban amfanin gona a Zabarmari.

Majiyoyi a rahoton sun bayyana cewa an "zagaye manoman ne kuma yan bindigan suka yi musu yankan rago," Hassan Zabarmari, tsohon shugaban manoman shinkafa a jihar Borno, ya bayyana ta wayar tarho.

Ya kara da cewa: "An kai wa manoman hari ne a gonan shinkafan Garin-Kwashebe, kuma bisa rahoton da muke samu da ranan nan, kimanin 40 cikinsu aka kashe."

Amma muna samun wasu rahotanni daban kan adadin wadanda aka kashe - wasu sun ce manoman da aka yanka sun kai 50."

Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun yiwa manoma sama 40 yankan rago a jihar Borno
Yanzu-yanzu: Yan Boko Haram sun yiwa manoma sama 40 yankan rago a jihar Borno
Source: Original

Saurarin karin bayani...

Source: Legit

Online view pixel