Yanzu yanzu: 'Yan Boko Haram sun yi wa manoman shinkafa 44 yankan rago a Borno

Yanzu yanzu: 'Yan Boko Haram sun yi wa manoman shinkafa 44 yankan rago a Borno

- Yan Boko Haram sun kashe manoma 44 a garin Zabarmari da ke Jihar Borno

- Rahotanni sun ce 'yan ta'addan sun afkawa manoman yayin da suke aiki a gonakinsu ne

- Dan majalisar tarayya da kuma majiyoyi da dama daga garin sun tabbatar da afkuwar lamarin

Wasu da ake zargin mayakan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ne sun kashe manoman shinkafa a kalla guda 44 a yayin da suke gurbe amfanin gonarsu a cewar dan majalisa da wasu majiyoyi.

Majiyoyi daga Zabarmari, wani gari a Borno da ya yi fice wurin noman shinkafa sun sanar da Premium Times cewa an kai wa manoman hari ne a lokacin da suke aiki a gonakinsu da ke Garin Kwashebe.

Yanzu yanzu: An 'kashe' manoma fiye da 40 a Borno, in ji mahukunta
Yanzu yanzu: An 'kashe' manoma fiye da 40 a Borno, in ji mahukunta. Hoto daga @PremiumTimes
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Hisbah ta yi bincike ɗaki-ɗaki don kama masu baɗala a Kano (Hotuna)

An kai wa manoman hari ne a ranar Asabar a yayinda mutanen garin ke zaben shugabanin kananan hukumomi, karo na farko a cikin shekaru 13.

Majiyoyi sun ce "yan ta'adddan sun tattara manoman cikin kankanin lokaci an musu yankan rago."

Hassan Zabarmari, tsohon shugaban kungiyar manoman shinkafa a Jihar Borno, ya tabbatarwa majiyar Legit.ng afkuwar lamarin ta hirar wayar tarho.

"Abin bakin cikin ya faru misalin karfe 11 na safen yau," ya ce a ranar Asabar. "An kai wa manoman hari a gonakin shinkafarsu da ke Garin-Kwashebe a cewar rahotannin da muka samu da rana, an kashe kimanin 40 cikinsu."

KU KARANTA: Hotuna: Sojoji sun kashe 'yan bindiga, sun kwato makamai da alburusai da dama

Dan majalisa wakilai na tarayya, Ahmed Satomi, wanda ke wakiltan mazabar Jere shima ya tabbatar da afkuwar lamarin a hirar da ya yi da Premium Times.

"Abinda ya da faru yau a gonakin shinkafa na Zabarmari abin bakin ciki ne matuka," a cewarsa.

"An yi wa manoma da masunta kisar gilla. Kawo yanzu mun samu gawarwarki 44 daga gonakin kuma muna shirin musu jana'iza gobe idan Allah ya kai mu."

Dan majalisar ya ce an kaiwa manoman harin ne "saboda a ranar Juma'a sun kama wani dan Boko Haram da ya dade yana adabarsu."

Kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Borno, Edet Okon, bai amsa wayarsa ba da aka kira shi a daren ranar Asabar. Bai kuma amsa sakon WhatsApp da aka aike masa ba.

A wani labarin daban, kungiyar gwamnonin Arewa maso gabas, NEFG, ta koka kan abinda ta kira rashin adalci da gwamnatin tarayya ke mata a bangaren gine-ginen tituna a yankin ta.

Kungiyar wadda ta hada da gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno Gombe, Taraba da Yobe ta bayyana hakan ne a ranar Juma'a cikin sakon bayan taro mai dauke da sa hannun shugabanta, Gwamna Babagana Zulum a karshen taronta na 3 da aka yi a Yola babban birnin Jihar Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164