Yanzu-yanzu: Kotu ta baiwa Sanata ali Ndume beli
- Daga taimako, Sanata Ali Ndume ya kwashe kwanaki hudu cir a gidan yarin Abuja
- A ranar Juma'a, Alkali ya bada belinsa kuma nan kyautata zaton za'a sake shi
Babban kotun tarayya dake Abuja ta baiwa Sanata mai wakiltan Borno ta kudu, Ali Ndume, wanda aka tsare a kurkuku tun ranar Litinin beli, The Punch ta ruwaito.
Alkali Okon Abang a hukuncin da ya yanke ranar Juma'a ya ce ya yanke shawaran baiwa Sanata Ndume beli ne saboda tarihinsa na halayya mai kyau, amma ba dan uzurorin da ya gabatar ba.
Alkali ya bashi beli ne kafin kotun daukaka kara ta saurari karar da Ndume ya shiga ranar Litinin domin kalubalantar hukuncin jefa shi kotu kan gaza kawo Maina kotu.
Ya umurci Sanatan ya kawo wanda zai tsaya masa kuma ya kasance mazauni Abuja kuma mai dukiya a Abuja.
A cewar Alkali, wanda zai tsayawa Sanatan wajibi ne ya rantse cewa zai sadaukar da dukiyarsa idan Sanatan ya gudu.
Bayan haka, Alkalin ya umurci Sanatan ya sallama fasfot dinsa ga magatakardan kotun.
KU KARANTA: Yan bindiga sun budewa babban Sarkin Gargajiya wuta, sun kashe shi
KU KARANTA: NEGF: Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas ta yi taro a Jihar Adamawa
Bugu da kari, ya umurci Sanata Ndume ya yi alkawarin zai mika takardun daukaka kararsa kotun daukaka kara cikin kwanaki 10.
Alkali ya garkame Ali Ndume a kotu ne bayan wanda ya tsayawa a kotu, AbdulRashid Maina, ya gudu.
Maina, tsohon shugaban kwamitin gyaran lamuran fansho, yana gurfana a kotu kan zargin almundahanar makudan biliyoyi.
A ranar 18 ga Nuwamba, 2020, Alkali Abang ya janye belin da ya baiwa Maina kuma ya bada umurnin daureshi.
Bayan an nemi Maina an rasa, Alkali ya ce a garkame Ndume a kotu maimakonsa ko ya biya kudi N500m.
A bangare guda, Wata kotun majistare dake Wuse, Zone 6, ta yankewa wani mamban majalisar wakilan tarayya, Victor Mela, hukuncin zama a gidan yari na tsawon wata daya.
Amma kotun ta baiwa dan majalisar mai wakitan mazabar Billiri/Balanga, zabin biyan tara.
Rahotanni sun bayyana cewa kotun majistare ta kama dan majalisan da laifin rantsuwa kan karya yayinda yake cika takardan INEC gabanin zaben 2019.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng