Kisan manoma 44 a Borno: Gwamnatinmu ta yi iyakar kokarinta, Buhari
- Shugaba Buhari ya nuna alhininsa a kan kisan manoman shinkafa 40 da 'yan boko haram sukayi a Maiduguri
- A cewarsa, 'yan ta'addan sun yi kisan rashin hankali, inda suka yi wa manoma 44 yankan rago
- A ranar Asabar da safe, da misalin 11am, 'yan boko haram suka kai harin wata gonar shinkafa da ke Zabarmari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa a kan kisan manoman shinkafa a gonar Zabarmari da ke karamar hukumar Jere a jihar Borno, inda yace 'yan ta'addan basu da hankali.
"Na yi matukar takaicin kisan manoma masu kwazo da 'yan ta'adda suka yi a jihar Borno. Kowa a kasar nan ya ji takaicin wannan kashe-kashe na rashin hankali. Ina mika sakon ta'aziyya ta ga iyalan wadanda aka kashe, ina musu addu'ar samun rahama."
Shugaba Buhari ya ce gwamnati ta yi iyakar kokarinta na kawar da ta'addanci a kasar nan.
Premium times ta ruwaito yadda a kalla manoman shinkafa 44 suka rasa rayukansu sakamakon wadanda ake zargin 'yan boko Haram ne suka kai musu hari a ranar Lahadi, suna tsaka da girbin shukokinsu.
KU KARANTA: Batanci ga Annabi: An tsananta tsaro a kotun daukaka kara da ke Kano
Majiya daga Zabarmari, wurin da yayi fice a noman shinkafa, ya sanar da Premium times cewa an kai wa manoman hari lokacin da suke aiki a gonar Garin Kwashebe.
An kai wa manoman hari a ranar Asabar lokacin mazaunan jihar suna tsaka da zaben kananun hukumomi, a karo na farko, cikin shekaru 13.
Majiya daga manoman ta ce "Manoman suna kokarin gama girbin kenan, 'yan ta'addan suka yi musu yankan rago".
Hasan Zabarmari, tsohon shugaban manoman shinkafa na jihar Borno, ya tabbatar wa da premium times faruwar lamarin a waya.
KU KARANTA: Girgizar zukata: Hotunan masoya da suka gano mahaifinsu daya ana saura kwanaki aurensu
"Mummunan al'amarin ya faru ne da misalin karfe 11 na safiyar yau," kamar yadda yace a ranar Asabar.
"Sun kai wa monoman hari a gonar shinkafan Garin-Kwashebe, sannan yadda labarai suka zo mana tun da rana, kusan mutane 40 suka rasa rayukansu."
A wani labari na daban, Felicia Okpara, ta ce 'yan sanda sun cutar da ita saboda ta daga waya tana daukar bidiyon zanga-zangar EndSARS da matasa suka yi a Surulere da ke jihar Legas.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng