Da kudin baitul-mali Bukola Saraki ya mallaki gidajensa na Ikoyi inji EFCC

Da kudin baitul-mali Bukola Saraki ya mallaki gidajensa na Ikoyi inji EFCC

- EFCC tana zargin da dukiyar kasa Bukola Saraki ya mallaki wasu gidaje a Legas

- Hukumar ta na kotu ta na neman a bata dama ta raba shi da wadannan dukiyoyi

- Ana tuhumar tsohon Gwamnan cewa ya taba baitul-mali wajen sayen gidajensa

Hukumar EFCC tana zargin Bukola Saraki da laifin wawurar Naira biliyan 12 daga asusun gwamnatin jihar Kwara a lokacin da yake kujerar gwamna.

Wani wanda hukumar EFCC ta kawo ya bada shaida a gaban kotun tarayya da ke zama a Legas, ya fadi yadda Bukola Saraki ya taba dukiyar gwamnatin jiha.

Olamide Sadiq dake aiki da hukumar EFCC a matsayin mai bincike, ya shaida wa kotu cewa da kudin gwamnatin Kwara Saraki ya saye gidaje a garin Ikoyi.

KU KARANTA: Bincike ya bankado ta’adin da Ma’aikatan Gwamnati suka tafka

Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto cewa Olamide Sadiq ya gabatar da wasu takardu dake nuna yadda tsohon gwamnan ya taba baitul-malin jihar Kwara.

A cewar Sadiq, an dauki kudi daga asusun gwamnatin jihar Kwara, an zuba cikin wani akawun a daya daga cikin fitattun bankuna da Bukola Saraki ya mallaka.

Alkali mai shari’a, Mohammed Liman ya saurari bayanin Sadiq, kamar yadda EFCC ta fitar da jawabi ta bakin mai magana da yawun bakinta, Wilson Uwujaren.

Gidajen da Bukola Saraki ya saya a Legas suna kan titin MacDonald ne a unguwar Ikoyi. Wadannan kadarori na tsohon gwamnan sun zama masa ala-ka-kai.

Da kudin baitul-mali Bukola Saraki ya mallaki gidajensa na Ikoyi inji EFCC
Bukola Saraki Hoto: Naijanews
Source: UGC

KU KARANTA: Matasan da su kayi wa Annabi Muhammad SAW sun koma kotu

A cewar EFCC, Saraki ya wawuri kudin ne ta hannun wani daga cikin hadiminsa, Abdul Adama.

Jami’an hukumar EFCC sun buga alama a jikin gidajen tsohon shugaban majalisar dattawan. Yanzu ana kotu, an fara shari’ar raba fada tsakanin EFCC da Saraki.

A ranar Juma'a kun ji cewa 'yan Sanda sun cafke wasu mutanen Najeriya uku da su ka addabi mutane da kamfanoni a kasashe akalla 150 da damfara da zamba.

Interpol da ‘yan Sandan Najeriya ne su kayi nasarar ram da wadannan miyagun ‘Yan Yahoo-Yahoo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel