Hukumar Hisbah ta hana amfani da kalmar ‘Black Friday’a Kano

Hukumar Hisbah ta hana amfani da kalmar ‘Black Friday’a Kano

- Hukumar Hisbah ta aike wa wata tasahr radiyo da takardar gargadi kan batun Black Friday

- An dade ana bikin 'Bakar Juma'a' inda manyan kantina ke ware ranar domin gwanjon kayayyakinsu musamman yayin da shekara ke ƙarewa

- Hisbah ta nuna cewa Black Friday barazana ce ga tsaro da zaman lafiyar jihar Kano kasancewar Musulmai sun fi yawa kuma suna girmama ranar

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bukaci wata tashar radiyo da ta daina amfani da Kalmar ‘Black Friday’ wato "Baƙar Juma'a a jihar, jaridar The Cable ta ruwaito.

Black Friday kan kasancewa ranar Juma’a ta hudu a watan Nuwamba inda yan kasuwa ke zabtare farashin kayayyaki ga abokan cinikinsu gabannin bikin Kirsimeti.

A wata wasika mai kwanan wata 26 ga watan Nuwamba zuwa ga manajan tashar Cool FM a Kano, Abubakar Ali, wani jami’in Hisbah a madadin kwamanda Janar, ya ce mafi akasarin mazana jihar Musulmai ne wadanda ke kallon ranar a matsayin rana mai tsarki.

Hukumar Hisbah ta hana amfani da kalmar ‘Black Friday’a Kano
Hukumar Hisbah ta hana amfani da kalmar ‘Black Friday’a Kano Hoto: @thecableng
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Da gangan muka rufe matatun mai, In ji shugaban NNPC

Ali ya fada ma manajan cewa a kan haka, tashar radiyon ta daina amfani da Kalmar “Black Friday” ba tare da bata lokaci ba.

Takardar ta kuma nuna cewa Black Friday barazana ce ga tsaro da zaman lafiyar jihar Kano.

Hukumar a cikin wasikar ta ce:

"Muna bayyana damuwa kan ayyana Juma'a a matsayin Black Friday, kuma ya kamata a fahimci yawancin al'ummar Kano Musulmi ne da suka ɗauki Juma'a babbar rana."

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Kotu ta baiwa Sanata ali Ndume beli

"Don haka Hisbah na son a daina kiran Juma'a Black Friday cikin gaggawa, kuma a kula cewa jami’an hukumar za su kasance a girke domin kula da lamura domin gudun afkuwar kowani irin abu na rashin da’a da kuma wanzar da zaman lafiya da aminci a jihar. Muna fatan alkhairi."

A gefe guda, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kashe kimanin bilyan 1.8 don daukan nauyin wasu dalibai a jami'o'in Najeriya.

Ya yi zargin cewa tsohon gwamnan jihar, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi watsi da su, The Nation ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel