Ganduje: Na biya N1.8bn kan daliban da Kwankwaso ya yi watsi da su

Ganduje: Na biya N1.8bn kan daliban da Kwankwaso ya yi watsi da su

- Gwamnatin jihar Kano ta taya daliban da ta dau nauyin karatunsu murnan kammalawa

- Biyu cikin daliban sun kammala da matsayin 1st Class, yayinda sauran suka gama da 2nd

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Laraba ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kashe kimanin bilyan 1.8 don daukan nauyin wasu dalibai a jami'o'in Najeriya.

Ya yi zargin cewa tsohon gwamnan jihar, Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi watsi da su, The Nation ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana sunayen jami'o'in matsayin Jami'ar Amurka dake Najeriya AUN Yola; Jami'ar Alqalam, Jami'ar ilmin fasaha Bells,dake Ota; da kuma Jami'ar Igbinideon dake Okada.

Ganduje yayi jawabi ne yayin gabatar shahada ga dalibai 20 da suka kammala karatu a taron majalisar zartaswar jihar Kano.

Daga cikin daliban AUN 20, biyu sun fito da matsayi na farko; Abubakar Bala Musa da Rabi’u Ibrahim Kabiru.

A jawabin da sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar, ya saki, ya ce an kai daliban karatu jami'o'in lokacin gwamnatin Kwankwaso, amma kashi 10 kadai aka biya na kudin makarantansu.

KU KARANTA: Ba zamu yarda yan bindiga suna binmu gida sun sacemu ba, Zulum

Ganduje: Na biya N1.8bn kan daliban da Kwankwaso ya yi watsi da su
Ganduje: Na biya N1.8bn kan daliban da Kwankwaso ya yi watsi da su Hoto: Presidency
Asali: UGC

KU DUBA: Dole a kare Jami’o’i da sauran wurare daga hare-haren ‘Yan bindiga inji Majalisa

Ganduje yace: "Lokacin da muka hau mulki a 2015, mun gaji sama da dalibai 1,150 daga gwamnatin Rabi'u Musa Kwankwaso, ta dau nauyin karatunsu a ciki da wajen Najeriya."

"An fada mana cewa an biya dukkan kudin makaranta, ashe karya ne."

"Amma tun da yaranmu ne, mun biya kashi 80 na kudi domin su kammala karatunsu,"

A bangare guda, wasu yan aji karshe a makarantan sakandare sun fita daga makaranta a gabashin kasar Kenya ranar Laraba suna masu cewa gaskiya sun gaji da karatu.

A cewar jaridar Standard, wadanda yara yan makaranta Matungulu Boys Secondary School ne. Yanzu dalibai 36 kadai suka rage a makarantan.

Shugaban makarantan yace daliban na fuskantar ukubar laifukan da suka aikata ne shi yasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel