Da gangan muka rufe matatun mai, In ji shugaban NNPC

Da gangan muka rufe matatun mai, In ji shugaban NNPC

- Shugaban kamfanin man fetur na NNPC, Mele Kyari ya bayyana cewa da gangan suka rufe matatun man kasar

- A cewar Kyari, ayyukan barayi na fasa bututun mai ya sa ba sa iya tura danyen mai da matatun za su tace

- Ya ce masu fasa bututu sun ja wa NNPC asarar Naira biliyar 43 a wata shidan farko na 2020 kuma a duk wata barayi na fasa bututun mai sau 80

Manajan Darakta na kamfanin man fetur din Najeriya (NNPC), Mele Kyari, a ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba, ya ce an rufe matatun man kasar ne duk da kudaden da ake kashewa na gyaransu saboda fasa bututun mai da barayi suka yi.

Ya ce hakan ya sa bututan ba sa iya tura danyen mai da matatun za su tace.

Hakan na kunshe ne a daftarin kasafin kudin 2021 da Kyari ya gabatarwa da kwamitin majalisar wakilai.

Da gangan muka rufe matatun mai, In ji shugaban NNPC
Da gangan muka rufe matatun mai, In ji shugaban NNPC Hoto: @NNPCgroup
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Kyari ya ce da gangan aka rufe matatun man saboda ba za su iya ci gaba da aiki ba.

Ya ce a halin yanzu, layin bututun mai na Excravos da ake kula wa kamfanin da shi ne kadai ke cikin koshin lafiya.

A cewarsa, babu alfanu a ci gaba da gudanar da matatun, ana kashe musu kudade masu yawa ba tare da ana cin moriyarsu ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Kotu ta baiwa Sanata ali Ndume beli

“Misali, idan mutum zai gudanar da matatun main a Kaduna da Warri, yana bukatar samar da gangar mai 170,000 a kulla yaumin saboda matatun biyu su yi aiki kasha 70 cikin dari” in ji shi.

Kyari ya bayyana cewa a yanzu haka, suna da bututun mai sama da kilomita 5,000 tare da manyan ma’ajin 13, wanda a cewarsa dole a basu kariya sosai don hana ayyukan yan fashi.

“Kuma ina iya fada maku cewa a yau baya ga layin bututun Atlas Cove zuwa Ibadan da kuma na Port Harcourt zuwa Abia, babu ko guda daga cikin wadannan bututun da aka yi wa gyara.

“Ba za mu iya tura mai cikin wadannan bututun ba saboda tsufa, amma yawan barnar masu fasa bututun ya zarce tunani,” in ji shi.

Ya ce kimanin naira biliyan 43 aka rasa sakamakon ayyukan barayin maid a masu fasa bututu a watan Janairu da Yunin 2020. Cewa duk wata barayi na fasa bututun mai sau 80.

A cewarsa wannan ce ta sa kamfanin ya gwammace ya rika dakon mai daga manyan ma’aijiya zuwa sassan Najeriya.

Ya kara da cewa kamfanin zai kashe biliyan N314.9 a kan ayyuka a 2021 sabanin biliyan 444.75 na 2020.

Kyari ya kuma sanar da kwamitin cewa kamfanin ya rasa kudaden shiga da ma wasu ayyukansa sakamakon bullar annobar korona.

Durkushewar tattalin arziki da dokar kulle sun karya farashin mai tare da raguwar hakarsa, baya ga karkata da duniya ta fara yi suwa ga makamashi na zamani.

Raguwar kudaden shiga sun tilasta wa NNPC rage kudaden da take kashewa zuwa kashi 40%, kasancewar ta kasa sauke wasu nauyin da suka rataya a wuyanta na tara kudade da aikace-aikace.

KU KARANTA KUMA: Fatara, rashin biyan albashi da rigimar shugabanci suke addabar PDP inji APC

A cewarsa, duk da cewa Najeriya na kokarin kara yawan kudaden shiganta ta bangaren mai, ita ma kamar sauran kasashe ta rungumi amfani da makamashi na zamani.

Saboda haka ya roki Majalisar Tarayya ta taimaka ta amince da kudurin dokar man fetur (PIDB).

A wani labarin, hukumar NERC mai sa ido a harkar wutar lantarki a Najeriya, ta sanar da jama’a game da zaman da za ayi domin duba farashin shan wuta a kasar.

Daily Trust ta rahoto cewa NERC za ta yi wannan zama karo na biyu kenan a shekarar nan ta 2020.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel