Yanzu-yanzu: Kotu ta bada umurnin garkame dan majalisar wakilai a kurkuku

Yanzu-yanzu: Kotu ta bada umurnin garkame dan majalisar wakilai a kurkuku

Wata kotun majistare dake Wuse, Zone 6, ta yankewa wani mamban majalisar wakilan tarayya, Victor Mela, hukuncin zama a gidan yari na tsawon wata daya.

Amma kotun ta baiwa dan majalisar mai wakitan mazabar Billiri/Balanga, zabin biyan tara.

Rahotanni sun bayyana cewa kotun majistare ta kama dan majalisan da laifin rantsuwa kan karya yayinda yake cika takardan INEC gabanin zaben 2019.

Ya yi rantsuwa har sau uku, cewa shi ba dan wata kasa bane daban yayinda ya mallaki fasfot na Birtaniya.

Hukumar yan sanda ta shiga aiwatar da umurnin a Abuja.

Yanzu-yanzu: Kotu ta bada umurnin garkame dan majalisar wakilai a kurkuku
Yanzu-yanzu: Kotu ta bada umurnin garkame dan majalisar wakilai a kurkuku
Source: Twitter

Karin bayani na nan tafe....

Source: Legit

Online view pixel