Tsohon direkta ya tsallake rijiya da baya yayinda 'yan bindiga suka afka musu a Abuja

Tsohon direkta ya tsallake rijiya da baya yayinda 'yan bindiga suka afka musu a Abuja

- Yan bindiga sun tare wata mota da ke dauke da wani tsohon direkta a Mararaban Kuchichanchan da ke Kwali Abuja

- Bata garin sun rotsa gilashin motar da dutse a yayin da suka lura tsohon direktan zai fice daga motar ya tsere

- Harbin da suka yi da dutse ya yi sanadin yi wa tsohon direktan mummunan rauni da ya yi sanadin sumarsa nan take kwance cikin jini

Wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace mutane hudu a Mararaban Kuchichanchan da ke Pai road a karamar hukumar Kwali da ke Abuja.

Wani mazaunin unguwar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce wani tsohon direkta ya sha da kyar da raunika da 'yan bindigan suka masa da duwatsu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce lamarin ya faru ne misalin karfe 5 na yammacin ranar Laraba inda wasu 'yan bindigan da ba a tabbatar da adadinsu ba suka bullo daga cikin daji da bindigu suka tare wata mota da ke dauke da direktan mai murabus.

Tsohon direkta ya tsallake rijiya da baya yayinda 'yan bindiga suka afka musu a Abuja
Tsohon direkta ya tsallake rijiya da baya yayinda 'yan bindiga suka afka musu a Abuja. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yan bindiga sun afka wasu kauyukan uku a Zamfara, sun kashe uku, mazauna gari sun tsere

Ya ce direktan da ke zaune a gaban mota ya yi yunkurin bude kofa ya tsere amma daya daga cikin yan bindigan ya yi amfani da katon dutse ya fasa gilashin gaban motar ya bugi direktan da dutsen.

Majiyar ya ce 'yan bindigan sun sake tare wata mota kirar Hilux da ke zuwa daga baya suka sace mutum daya da direban motan zuwa cikin daji.

"A lokacin da suke harkallarsu ne wani mai babur shima ya taho amma suka yi amfani da adda suka masa duka suka shiga da shi daji," in ji shi.

KU KARANTA: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya

Majiyar Legit.ng ta gano cewa yan bindigan sunyi kokarin tafiya da direktan amma suka kyalle shi bayan sun gano cewa ya suma a kwance cikin jininsa.

Daga bisani an kai direktan wani asibiti a Gwagwalada aka yi masa magani har ma an sallame shi a ranar Laraba da safe.

A bangarensu, rundunar yan sanda ta tabbatar da sace mutum uku a Pai-Leleyi road a karamar hukumar Kwali.

A cewar sanarwar da kakakin yan sanda, ASP Maryam Yusuf ta fitar, rundunar ta fara bincike don ceto wadanda aka yi garkuwan da su inda ta kara da cewa rundunar ta ceto mutum 19 daga hannun masu garkuwa a Kwali.

A wani labarin, tsohon shugaban majalisar dattawar Najeriya, Sanata Joseph Wayas, yana wata asibiti a birnin Landan sakamakon rashin lafiya da ya ke fama da ita kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sanata Wayas shine shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu daga shekarar 1979 zuwa 1983 a lokacin da marigayi Alhaji Shehu Shagari ke shugaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel