Rundunar yan sanda ta yi martani yayinda yan bindiga suka sace mutum uku a Abuja

Rundunar yan sanda ta yi martani yayinda yan bindiga suka sace mutum uku a Abuja

- Rashin tsaro a babbar birnin tarayya, Abuja na kara tabarbarewa a kulla-yaumin

- A wannan karon, yan sanda ne suka sanar da batun sace wasu mutane

- Wata sanarwa daga hukumar yan sanda ya ce an yi garkuwa da mutane uku bayan jami’anta sun dakile wani yunkuri na garkuwa da mutane 19

Wasu mutane da ake zaton yan fashi ne sun yi garkuwa da mutane uku a babbar birnin tarayya, Abuja.

Rundunar yan sandan birnin tarayya ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Legit.ng ta gani a ranar Alhamis, 26 ga watan Nuwamba.

Sai dai sanarwar, ta bayyana cewa jami’an sun dakile wani yunkuri na garkuwa da mutane 19, amma abun bakin ciki shine yan bindigan sun yi awon gaba da wasu mutum uku.

Rundunar yan sanda ta yi martani yayinda yan bindiga suka sace mutum uku a Abuja
Rundunar yan sanda ta yi martani yayinda yan bindiga suka sace mutum uku a Abuja Hoto: @AbujaGSC
Asali: Twitter

A cewar sanarwar, lamarin ya afku ne a shahararriyar hanyar nan ta Pei-leilei kusa da yankin Kwali a babbar birnin tarayya, jaridar The Punch ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Maina: Kotu ta tsayar da ranar Juma’a don yanke hukunci kan bukatar belin Ndume

Rundunar ta sanar da ‘yan Najeriya cewa ana nan ana kokarin ganin an ceto mutane ukun da ke a hannun yan bindigar.

Wani bangare na sanarwar ya zo kamar haka:

“Rundunar na sake ba jama’a tabbacin jajircewarta na daukar matakan yaki da laifuka a kan lokaci domin tabbatar tsaron rayuka da dukiyoyi a birnin tarayya gabannin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.”

KU KARANTA KUMA: Ina asibiti, bani da lafiya - Abdulrasheed Maina ya maida martani ga hukuncin Kotu

A wani labarin kuma, mun ji cewa rundunar Sojojin Najeriya karkashin atisayen Hadarin Daji ta hallaka yan bindiga 82 a jihohin Katsina da Zamfara kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Rundunar ta kuma kawar da yan ta'adda 67 a dajin Birnin Kogo da ke Katsina, sun kuma kawar da wasu 15 a dajin Ajjah da ke Zamfara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel