Taiwo Olowo: Basaraken da aka dade ba a yi mai arziki irinsa ba a Legas, yadda ya tara kudinsa
- Taiwo Olowo, fitaccen basarake ne mai tarihin dumbin dukiya a jihar Legas
- Har yanzu akwai yanki a tsibirin Legas da ke amsa sunan hamshakin dan kasuwar
- Sannan mahaifinsa babban dan siyasa da gogayya ne tun zamanin turawan mulkin mallaka
Mutane da dama suna mamakin yadda wani fitaccen titi a tsibirin Legas yake amsa sunan Taiwo Olowo. Yana daya daga cikin masu dukiya a jihar, Wikipedia ta sanar da 1781 a matsayin shekarar da aka haifeshi a Isheri, sannan mahaifinsa, Oluwole, sarki ne.
Olowole babban mai safarar bayi ne, kuma hamshakin dan siyasa ne a lokacin turawan mulkin mallaka. A 1840, an nada shi a matsayin protégé na Oba Kosoko, wanda yayi zamani a jihar Legas tsakanin 1845 zuwa 1851.
Taiwo yayi amfani da kusancinsa da Sarkin don ya kara fadada kasuwancinsa, wanda ya hada hannun jari da 'yan kasuwan turawa.
KU KARANTA: Mahaifiya ta rasu washegarin rasuwar dan ta daya tilo a duniya
Kamar yadda Wikipedia ta bayyana, ba a tabbatar da ko ya bar Legas ya tafi Kosoko ne don daura Oba Akitoye da turawan mulkin mallaka suka yi ba, ko kuma ba hakan ba.
Dukiyar Taiwo ta fadada ne bayan ya gabatar da gwamna Glover, wanda ya kara masa kaimi a kan kasuwanci da Messrs GL Gaisers. Bayan ya samu wannan darajar ne ya zama Baba Isale na Isheri, wanda yake wakiltar mutanen Isheri.
Sai ya zamanto shine kadai yake da damar yin titina a duk birane. Bayan rasuwar Oshodi Tapa, dan kasuwar sarkin Kosoko ya maye gurbinsa da kuma matsayinsa na mulki.
Taiwo ya rasu a ranar 20 ga watan Fabrairun 1901, yana da shekaru 120. Amma har yanzu babu wata takarda da ta tabbatar da an haifeshi a 1781.
KU KARANTA: Hukumar kurkukun Kuje ta saka takunkumi, ta hana 'yan majalisa ganin Ndume
A wani labari na daban, a kalla 'yan bindiga 67 dauke da miyagun makamai suka sheka lahira yayin da wasu suka samu rauni sakamakon ragargazar da dakarun sojin saman rundunar Operation Hadarin Daji a dajin Birnin Kogo a Katsina.
Duk a lokaci daya, an samu kashe wasu 'yan bindiga 15 a dajin Ajjah da ke jihar Zamfara sakamakon harin sojin saman. An kai dukkan samamen ne a ranar 23 ga watan Nuwamban 2020 bayan bayanan sirrin da dakarun sojin suka samu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng