DHQ ta kaddamar da manhajar AFNDSP domin sojoji da iyalansu

DHQ ta kaddamar da manhajar AFNDSP domin sojoji da iyalansu

- Hedikwatar rundunar tsaro (DHQ) ta samar da wata manhaja domin amfanin sojoji da iyalansu

- Sabuwar manhajar za ta taimakawa jami'an sojoji da iyalansu da ke rayuwa a cikin bariki wajen sadarwa da siyayya

- Gwamnatin tarayya ce ta fara zuwa da tsarin kirkirar manhajar tare da hadin gwuiwar ma'aikatar sadarwa

Babban hafsan rundunar tsaro ta kasa (CDS), Janar Abayomi Olanisakin, ya kaddamar da manhajar AFNDSP (Armed Forces of Nigeria Digital Service Platform) domin amfanin jami'an soji da iyalansu.

Wani kamfanin sadarwa mai lakabin KNL (Keywares Networks Limited) ne ya yi aikin tsarawa da gina manhajar a karkashin wani tsari na sadarwa AFN.

Gwamnatin tarayya ce ta fara kirkirar tsarin a karkashin ma'aikatar sadarwa domin dora manhajar akan zango mai nisan 700MHz.

KARANTA: An ci moriyar ganga: Ko kadan Buhari bai damu da arewa ba yanzu; ACF da NEF sun aika sako

Da yake jawabi yayin kaddamar da tsarin, Janar Olanisakin, wanda Air Vice Marshal Jomo Osahor ya wakilta, ya ce an bawa AFN kwangilar aikin saboda kwarewarsu a bangaren sadarwa.

DHQ ta kaddamar da manhajar AFNDSP domin sojoji da iyalansu
DHQ ta kaddamar da manhajar AFNDSP domin sojoji da iyalansu
Asali: Twitter

A cewarsa, AFN ta dora manhajar a kan zangon mai nisan 700MHz na gwamnatin tarayya domin tabbatar da sadarwa mai nagarta ga sabuwar manhajar.

Ya ce manhajar ta kunshi wasu cibiyoyin sadarwa na rundunar soji (Defcom), 'E-Mammy Market,' tsarin kula da koyo da koyarwa, da kuma na kula da makarantu.

Kazalika, ya kara da cewa za'a kara wasu cibiyoyin sadarwa guda uku a kan manhajar a nan gaba.

KARANTA: Buhari ya tsame rukunin wasu ma'aikata daga biyan haraji

Taron kaddamar da manhajar ya samu halartar wakili daga ofishin ministan sadarwa, Injiniya Bamidele Sakariyau, da Farfesa Yakubu Ochefu, wanda ya yi magana amadadin mahaifiyarsa, shugabar matan da suka fara kafa kasuwa a barikin sojoji.

Wakilin Janar Olanisakin ya gwada manhajar yayin taron ta hanyar yin kira da kuma yin siyayya daga kasuwar da ke cikin barikin Mogadishu, Abuja, ta hanyar amfani da cibiyar 'e-Mammy'.

A kwanakin baya ne Legit.ng ta rawaito cewa birgediya janar (mai ritaya), Abubakar Sa'ad, ya shigar da karar ilahirin rundunar soji a gaban kotun ma'aikata (NIC) domin kalubalantar yi masa ritayar dole.

Sauran wadanda mai korafin ya ambata a cikin takardar shigar da kara sun hada da, babban hafsan rundar soji; Laftanal Janar Tukur Buratai, shugaban rundunar tsaro; Janar Abayomi Olanisekin, da kuma ministan tsaro; Bashir Salihi Magashi, da kuma majalisar koli da rundunar soji.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng