Mutumin da matarsa ta haifi yan uku ya koka, ya roki yan Najeriya su kawo masa tallafi
- Wasu ma’aurata yan Najeriya sun haifi yan uku amma rayuwa ta masu wuya sakamakon annobar korona
- Ma’auratan, wadanda suka haifi da daya kafin yan ukun, suna kira ga yan Najeriya a kan su kawo masu dauki
- Mijin ya ce ya rasa aikinsa a matsayin mataimaki a ofis sannan a yanzu yana aikin leburanci a duk inda ake aikin gini
Wasu ma’auratan Najeriya wadanda suka haifi yan uku kwanan nan sun bukaci mutane da su kawo masu dauki domin rayuwa ta yi masu wahala.
Da yake magana a Legit TV, Emmanuel Adah ya ce ya rasa aikinsa a matsayin mataimaki a ofis a lokacin annobar korona.
Ya ce ya shiga alhini a lokacin da matarsa ta bayyana masa sakamakon gwajin da aka yi mata don gano abunda take dauke da shi, inda ya kara da cewa ya bukaci ta sake wani gwajin amma duk labarin daya ne
Matar, wacce ta haihu ta hanyar tiyata, ta ce bata yi bakin cikin haihuwar yan uku ba duk da wuyan rayuwa da suke ciki a yanzu.
KU KARANTA KUMA: Tsaida sunnah: Kebbi ce jihar da ta fi kowacce yawan maza masu auren mata 2 a Nigeria
A cewar ma’auratan, har yanzu basu gama biyan kudin asibitin da aka yi mata aiki ba.
Emmanuel yace yana zuwa wuraren da ake aikin gini domin yin leburanci don sama wa iyalinsa abubuwan bukata.
A cewarsa, shi da matarsa sun tsara haihuwar karin da daya bayan haihuwar na farko, amma sai Allah ya azurta su da yan uku a maimakon haka.
KU KARANTA KUMA: Ka fito da kanka don kare Ndume daga wannan tozarcin, dan uwan Maina ya roke shi
A wani labarin, magidanci ya yasar da matarsa da ke jego, Evelyn, a wani asibitin kudi da ke Okpoko, karamar hukumar Ogbaru da ke jihar Anambra, inda ta haifi yan uku.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa tuni ma’auratan suka haifi yara hudu wadanda aka cire daga makaranta saboda rashin kudin biyan makarantar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng