Tsaida sunnah: Kebbi ce jihar da ta fi kowacce yawan maza masu auren mata 2 a Nigeria

Tsaida sunnah: Kebbi ce jihar da ta fi kowacce yawan maza masu auren mata 2 a Nigeria

- Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka ba auren mata da yawa muhimmanci

- Da zaran dai mutum ya mallaki rufin asirin da zai iya duba mace fiye da daya toh baya shakkar kara aure musamman a yankin arewacin kasar

- Kebbi, Katsina da Kaduna ne kan gaba a jihohin da maza ke auren mata fiye da guda daya

Auren mace fiye da guda daya abune da ya zama ruwan dare a Najeriya domin mutane da dama sun yarda cewa babu wani aibu dake tattare da tara mata idan har mutum na da halin daukar nauyin matan nasa na sunnah.

A kan haka, Legit.ng ta tattaro maku jihohin Najeriya inda maza daga shekaru 15 zuwa 49 suka mallaki akalla matan aure guda biyu.

KU KARANTA KUMA: Ka fito da kanka don kare Ndume daga wannan tozarcin, dan uwan Maina ya roke shi

1. Kebbi: 27.3%

Jihar Kebbi ce ke da mafi yawan maza masu matan aure fiye da biyu. Alkaluman na a kan kaso 27.3 cikin 100.

Tsaida sunnah: Kebbi ce jihar da ta fi kowacce yawan maza masu auren mata 2 a Nigeria
Tsaida sunnah: Kebbi ce jihar da ta fi kowacce yawan maza masu auren mata 2 a Nigeria Hoto: ABNA
Asali: UGC

2. Katsina: 26.3%

Katsina ce ke bin sahun Kebbi kuma yawan mazan da ke da matan aure fiye da guda biyu a wannan jiha shine kaso 26.3 cikin 100.

3. Kaduna: 26.2%

Kaduna ce ta uku a jerin jihohin da kaso 26.2 cikin 100.

Ga ci gaban jihohin daga na 4 kamar yadda shafin StatiSense ya wallafa a kasa:

KU KARANTA KUMA: Gwamonin Kudu: Ma'adanan yankinmu ake amfani da su amma an bar mu cikin mawuyacin hali

Ga yadda alkaluman ya zo bisa ga yankunan kasar:

A wani labarin, wani tsohon dan shekaru 72, Musa Abdullahi, ya shigar da kara wata kotu da ke yankin Gwagwalada, Abuja.

Ya nemi kotun da ta tursasa wata budurwa yar shekaru 18, Rukayya Idris, ta biya shi kudi N50,200 da ya kashe mata tunda ta ki yarda da tayin auren da yayi mata.

Abdullahi, wanda ke zama a Baure Anguwar Hausawa a Gwagwalada, ya fada ma kotu cewa ya nemi auren Rukayya a watan Yunin 2020 sannan ta amince za ta aure shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng