Gwamonin Kudu: Ma'adanan yankinmu ake amfani da su amma an bar mu cikin mawuyacin hali
- Gwamnonin kudu-kudu sun bukaci gwamnatin tarayya ta ba su damar amfani da ma'adanan yankinsu
- A cewarsu, hakan ne zai taimaka su bunkasa yankin nasu, don yanzu haka 'yan yankin suna mawuyacin hali
- Sun bukaci a mayar da matatun da ke Abuja da na jihar Legas yankinsu, don mutanen yankinsu su amfana
Gwamnonin kudu-kudu sun koka a kan rashin cigaban yankinsu, sun ce da dukiyar yankinsu ake bunkasa sauran yankuna, The Cable ta wallafa.
Ifeanyi Okowa, shugaban gwamnonin kudu-kudu, ya fadi hakan a ranar Talata a wani taron masu ruwa da tsaki da shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Ibrahim Gambari suka yi.
Abubuwan da suka tattauna a taron yana kun she a cikin wata takarda da Kelvin Ebiri, hadimin gwamnan jihar Rivers na musamman a kan harkar labarai ya fitar.
KU KARANTA: 2023: Fashola ya bayyana abinda ya dace APC tayi domin cigaba da mulki
Okowa ya yi jawabi a maimakon mutanen yankin, a taron da suka yi a gidan gwamnatin jihar Port Harcourt, babban birnin jihar, ya ce ya kamata a bai wa jihohin damar amfana da ma'adanansu don taimaka wa 'yan yankin.
A cewarsa, "Mun san irin albarkar da kasar nan take da ita, don haka wajibi ne a bai wa jihohi dama, yakamata a samar wa da jihohi yadda za su taimaki kansu da kansu.
"Abinda yafi muni shine yadda wasu 'yan Najeriya ba sa fahimta da kuma tausayi ga yankin kudu-kudu, musamman a kan yadda yankin yake a lalace.
"Don haka muna bukatar a dubi yankin, sannan a bai wa yankin damar amfani da ma'adanai da sauran kayan alatun da ke wurin don ciyar da yankin gaba."
KU KARANTA: Makashi ya fille wa mahaifi kai, ya halaka da har lahira a Kano
Gwamnonin sun nemi a sauya wa kamfanonin da ke sarrafa mai, daga Legas da Abuja zuwa yankin kudu-kudu. Sannan gwamnonin sun bukaci a kara gyara ofisoshin gefen ruwan Port Harcourt, Calabar da Warri don a bunkasa tattalin arzikin yankin kudu-kudu.
Sun kara da cewa, suna bukatar a sayar da matatu 2 da ke Port Harcourt da daya da ke Warri, wadanda suke kwasar dukiyar gwamnati.
A wani labari na daban, Sanata Ali Ndume, wanda ma'aikatan gidan gyaran hali na Kuje, Abuja, suka tafi da shi a ranar Litinin, a bisa umarnin babbar kotun tarayya dake Abuja, zai daukaka kara akan hukunci da aka masa yau, Talata.
Lauyan Ndume, Marcel Oru, ya ce za su daukaka karar ne yau a gaban kotun daukaka kara da ke Abuja.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng