An yi wa bakanike bulala 15 saboda satar waya a Kaduna

An yi wa bakanike bulala 15 saboda satar waya a Kaduna

- Kotu ta yanke wa matashi mai sana'ar kanikanci dan shekara 20 hukuncin bulala 15 da sharar harabar kotu saboda satar wayar salula

- Matashin mai suna Ibrahim Emmanuel ya afka gidan wani Leo Chidi ne ya sace masa waya a lokacin da ya ke barci

- Sai dai asirinsa ya tonu an cafke shi yayinda ya ke kokarin tserewa inda aka karbi wayar daga hannunsu aka kuma shigar da korafi ofishin yan sanda

Kotun majistare da ke Kaduna, a ranar Talata ta yankewa wani bakanike, Amos Dauda hukuncin bulala 15 saboda satar wayar salula kirar iPhone da aka kiyasta kudinsa ya kai Naira 150,000.

An gurfanar da wanda aka yanke wa hukuncin, mazaunin unguwar Barnawa, a Jihar Kaduna a kotun bisa zarginsa da laifin kutse da sata inda ya amsa laifinsa amma ya nemi kotu ta yi masa afuwa.

An yi wa makanike bulala 15 saboda satar iPhone a Kaduna
An yi wa makanike bulala 15 saboda satar iPhone a Kaduna. Hoto daga @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Abinda dan majalisar Burtaniya ya fadi game da Gowon ba gaskiya bane, in ji Shehu Sani

Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel, ya yankewa wanda ake zargin hukuncin bulala 15 sannan ya umurce shi ya share harabar kotun duk cikin hukuncinsa.

Ya kuma shawarci Emmanuel ya kasance mai hali na gari inda ya gargadi shi ya guji aikata laifuka domin kotu ba zata yi masa sassauci ba idan ta sake samunsa da laifi a nan gaba.

Tunda farko, mai shigar da kara Sufeta Leo Chidi ya shaidawa kotun cewa wani Stephen Francis ya shigar da korafi kan batun a ofishin 'yan sanda da ke Gabasawa a ranar 15 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya

A cewar mai shigar da karar, wanda aka yanke wa hukuncin ya shiga gidan wanda ya yi korafin yayin da ya ke barci ya sace masa wayarsa kirar iPhone da kudinsa ya kai Naira 150.

Chidi ya ce an kama wanda aka yanke wa laifin yayinda ya ke kokarin tserewa daga gidan sannan aka kwace wayar daga hannunsa.

Ya bayyana cewa laifin ya saba wa sashi na 257 da 271 na dokar Penal Code na Jihar Kaduna ta shekarar 2017.

A wani labarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam'iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel