Abinda dan majalisar Burtaniya ya fadi game da Gowon ba gaskiya bane, in ji Shehu Sani

Abinda dan majalisar Burtaniya ya fadi game da Gowon ba gaskiya bane, in ji Shehu Sani

- Sanata Shehu Sani ya karyata ikirarin da dan majalisar Burtaniya, Tom Tugendhat ya yi na alakanta Yakubu Gowon da wawushe kudin Najeriya

- Tugendhat yayin jawabi a majalisar Burtaniya ya yi ikirarin cewa tsohon Shugaban kasa na mulkin Soja Yakubu Gowon ya kashe kudi kimanin rabin na CBN da zai sauka daga mulki

- Sanata Shehu Sani ya karyata hakan inda ya ce babu alamar Gowon na da irin wannan arzikin tun daga saukarsa da mulki har zuwa yanzu kimanin shekaru 40

Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya yi wa ɗan majalisar Burtaniya, Tom Tugendhat's martani kan iƙirarin da ya yi na cewa tsohon shugaban mulkin soja Yakubu Gowon ya bar mulki da kuɗin da kai rabin abinda babban banki CBN ta mallaka.

Tugendhat ya yi wannan furucin ne yayin da ya ke tofa albarkacin bakinsa kan muhawarar yiwuwar hukunta gwamnatin Najeriya kan zargin keta harkokin bil adama yayin zanga zangar #EndSARS.

Dan majalisar Burtaniya sharri ya yi wa Gowon, Shehu Sani
Dan majalisar Burtaniya sharri ya yi wa Gowon, Shehu Sani. Hoto daga Guardian.ng/ yans.ng
Asali: UGC

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe masallata 5, sunyi awon gaba da liman da mutum 40 yayin sallar Juma'a a Zamfara

Shehu Sani ya ce wannan maganar ba gaskiya bane , inda ya ce Gowon ya sauka daga mulki ba tare da alamun ya tara arziki ba kuma ya cigaba da kasance a hakan fiye da shekaru 40 bayan saukarsa daga mulki.

Shehu Sani ya yi wannan martanin ne ta shafinsa na Twitter a ranar Talata 24 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya

Ga abinda ya rubuta:

"Janar Yakubu Gowon; Iƙirarin 'sata a CBN' ta ministan Afirka na ƙasar Birtaniya wadda Mista James Duddridge ya yi game da Janar Gowon ba komai bane illa tsantsagwaron ƙarya.

Gowon ya sauka daga mulki ba tare da alamun yana da arziki ba kuma ya cigaba da zama a hakan fiye da shekaru 40."

A wani labarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam'iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel