Kotu ta jefa magidanci cikin Kurkuku kan laifin satan Alewa da gajeren wando a kasuwa

Kotu ta jefa magidanci cikin Kurkuku kan laifin satan Alewa da gajeren wando a kasuwa

- Kan laifin satan gajeren wando, wani dan shekara 40 a duniya zai kwan 40 a gidan maza

- An gurfanar da shi gaban kotu dake birnin tarayya Abuja

Wata kotun Grade 1 dake Karu Abuja a ranar Talata ta yankewa wani mutum mai suna Kabiru Zakaru, hukuncin daurin kwanaki 40 a gidan gyara hali kan laifin satan Alewa da gajeren wando a kanti.

Alkalin, Inuwa Maiwada, ya yanke hukuncin ne bayan mutumin ya amsa laifinsa kan zargin sata da wuce iyaka da aka yi masa, The Nation ta ruwaito.

Amma Alkalin ya baiwa mutumin daman biyan taran N10,000 kuma da gargadin kada ya sake yin haka.

Bayan haka, Alkalin ya bada umurnin cewa a shigar da mutumin Islamiyya a Kurkuku saboda ya koyi ilimin addini don canza halinsa.

KU KARANTA: Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa ga Dr Isa Ibrahim ali Pantami

Kotu ta jefa magidanci cikin Kurkuku kan laifin satan Alewa da gajeren wando a kasuwa
Kotu ta jefa magidanci cikin Kurkuku kan laifin satan Alewa da gajeren wando a kasuwa
Asali: UGC

Lauyan da ya shigar da karan, Ayotunde Adeyanju, ya bayyanawa kotu cewa Manajan kantin FordMart Supermarket dake Karu, Abuja ya kai karan mutumin ofishin yan sanda ranar 6 ga Nuwamba.

Mai kantin ya ce a ranar, mutumin ya shiga ya debi goran ruwa biyu, jakar alewa, da gajerun wanduna uku, na kudi kimanin N4,500.

A cewarsa, mutumin ya biya kudin ruwa da alewan amma ya boye gajerun wandunan cikin rigarsa da niyyar sata.

"Amma bai sani ba, na'urar CCTV dake shagon ta daukeshi kuma shi da kansa ya amince da aikata hakan yayin bincikn yan sanda, " Adeyanju yace.

KU KARANTA: Ka ji tsoron Allah, ka martaba rantsuwar da ka yi ta kama aiki, ƙungiyar ACF ga Buhari

A wani labarin, rundunar Operation Fire Ball ta arewa maso gabas ta ragargaji 'yan bindiga 23, sannan ta kwashe wani abu mai fashewa a hannunsu, wuraren Ngamdu, kusa da Maiduguri.

Mukaddashin jami'in hulda da jama'a, Birgediya janar Benard Onyeuko, ya bayyana hakan a ranar Talata, inda yace wasu daga cikin 'yan bindigan sun sha ragargaza yayin kokarin amsar kudaden fansa daga hannun iyalan wadanda aka yi garkuwa dasu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel