Soji sun kashe mayakan Boko Haram 23, sun cafke kwararren mai hada bam

Soji sun kashe mayakan Boko Haram 23, sun cafke kwararren mai hada bam

- Rundunar Operation Fire Ball suna cigaba da samun nasarar ragargazar 'yan ta'adda a Maiduguri

- Rundunar ta samu nasarar kashe 'yan ta'adda 23, wurin ceto wasu mutane 5 daga hannun 'yan Boko Haram

- Kamar yadda mukaddashin jami'in hulda da jama'a, Birgediya janar Benerd Onyeuko ya tabbatar

Rundunar Operation Fire Ball ta arewa maso gabas ta ragargaji 'yan bindiga 23, sannan ta kwashe wani abu mai fashewa a hannunsu, wuraren Ngamdu, kusa da Maiduguri.

Mukaddashin jami'in hulda da jama'a, Birgediya janar Benard Onyeuko, ya bayyana hakan a ranar Talata, inda yace wasu daga cikin 'yan bindigan sun sha ragargaza yayin kokarin amsar kudaden fansa daga hannun iyalan wadanda aka yi garkuwa dasu.

A cewarsa, sojojin sun samu nasarar ceton wasu mata 2 da yara 3 a hannun 'yan Boko Haram, Vanguard ta wallafa.

A cewarsa, an samu bindigogi AK-47 guda 8, bindiga mai jigida, bindigogin yaki da sauran miyagun makamai bayan kashesu.

KU KARANTA: A taimaka a rage dukiyar aure ko 'yan mata za su samu shiga, budurwa ta roki iyaye

Soji sun kashe mayakan Boko Haram 23, sun cafke kwararren mai hada bam
Soji sun kashe mayakan Boko Haram 23, sun cafke kwararren mai hada bam. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Rundunar Operation Fire Ball suna cigaba da samun nasarar yin ayyuka tukuru a yankin. A cikin kankanin lokaci sun samu nasara mara misaltuwa.

Sakamakon ragargazar, sojoji 6 sun ji munanan raunuka, amma suna asibitin sojoji suna samun sauki.

Onyeuko ya roki mazauna yankin da su bai wa sojojin hadin kai, don samun damar sanin shige da ficen 'yan ta'addan da maboyarsu.

KU KARANTA: ASUU: 'Ya'yana 3 ne suke jami'o'in gwamnatin Najeriya, Ngige

A wani labari na daban, sojojin Najeriya sun dakatar da harin wasu 'yan bindiga a anguwar Sabon Birni da ke karamar hukumar Igabi a cikin jihar a ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba.

Gidan talabijin din Channels, sun ruwaito yadda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan.

Kwamishinan ya yaba wa rundunar a kan yadda ta mayar da harin da aka kai. Kamar yadda jaridar Channels ta ruwaito, fiye da mutane 11 ne suka rasa rayukansu a karamar hukumar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel