Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa ga Dr Isa Ibrahim ali Pantami

Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa ga Dr Isa Ibrahim ali Pantami

- Shugaban kasa ya jajantawa Sheikh Isa Ibrahim Pantami

- An yi jana'izar Aisha a ranar Talata a masallacin Annur da ke Wuse 2 a Abuja bayan sallar Zuhr.

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika sakon ta'ziyyarsa ga Ministan sadarwa, Dr Isa Ibrahim Ali Pantami, bisa rashin diya da yayi ranar Litinin, 23 ga Nuwamba, 2020.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana cewa Buhari daga samun labarin mutuwar Aisha ya kira Dr Isa Pantami a waya yayi masa jaje.

Ya yi addu'a Allah jikanta kuma ya karawa iyalan Minista Pantami hakuri.

Yace: "Shugaba Buhari ya kira Ministan da yammacin Litinin, inda ya jajantawa dukkan iyalansa bisa wannan rashi."

"Buhari ya yi addu'a Allah ya jikanta kuma ya azurta ta da Jannatul Firdausi."

KU KARANTA: Soji sun kashe mayakan Boko Haram 23, sun cafke kwararren mai hada bam

Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa ga Dr Isa Ibrahim ali Pantami
Buhari ya aika sakon ta'aziyyarsa ga Dr Isa Ibrahim ali Pantami
Asali: Facebook

KU KARANTA: Ka ji tsoron Allah, ka martaba rantsuwar da ka yi ta kama aiki, ƙungiyar ACF ga Buhari

Mun kawo muku rahoton cewa Aishah Isa Ali (Amal), diyar Ministan Sadarwa ta tattalin arziki na zamani, Shiekh Isa Ali Pantami ta rasu.

Amal wacce ke da shekaru 13 a duniya ta rasu ne a ranar Litinin 23 ga watan Nuwamban 2020 kamar yadda Sheikh Pantami ya sanar ta shafinsa na Twitter.

An yi jana'izar ta a ranar Talata a masallacin Annur da ke Wuse 2 a Abuja bayan sallar Zuhr.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel