Maina: Ndume ya kwana a gidan kurkuku, ya bayyana matakin da zai dauka

Maina: Ndume ya kwana a gidan kurkuku, ya bayyana matakin da zai dauka

- Jiya da misalin karfe 4 na yamma aka tafi da Sanata Ndume gidan gyaran hali da ke Kuje, Abuja

- Amma kuma lauyansa ya ce ba a basu wasu takardu da suka bukata ba domin su daukaka kara

- A yau ne ake sa ran za a cigaba da shari'ar, wala Alla ko zai samu dama cika wani sharadi a sakeshi

Sanata Ali Ndume, wanda ma'aikatan gidan gyaran hali na Kuje, Abuja, suka tafi da shi a ranar Litinin, a bisa umarnin babbar kotun tarayya dake Abuja, zai daukaka kara akan hukunci da aka masa yau, Talata.

Lauyan Ndume, Marcel Oru, ya ce za su daukaka karar ne yau a gaban kotun daukaka kara da ke Abuja, Daily Trust ta tabbatar.

A cewarsa, ba a ba iwa Ndume damar jin ta bakinsa ba, sannan ba su bashi wasu takardu da ya bukata ba don ya kare kansa.

Maina: Ndume ya kwana a gidan kurkuku, ya bayyana matakin da zai dauka
Maina: Ndume ya kwana a gidan kurkuku, ya bayyana matakin da zai dauka. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Batan dabon Maina: Kotu ta bukaci a adana mata Sanata Ndume a gidan maza

Alkali Okon Abang, wanda shine ya bayar da wannan umarnin a kan Ndume, wanda ya tsaya wa tsohon shugaban PPRTT, Abdulrasheed Maina, da aka kama bayan Maina ya ki bayyana gaban kotu, bisa zargin cin kudin fansho na naira biliyan 2.

"Muna bukatar wasu takardu don gabatar da ita gaban alkali don kare Ndume," cewar lauyansa.

"Ba a yi mana adalci an bamu wannan damar ba, kafin kotu ta zartar da hukunci," cewarsa.

Wata majiya ta kusa da Ndume, ta ce an tafi dashi gidan gyaran halin da misalin karfe 4 na yammacin jiya.

KU KARANTA: Cunkoso: Bata-gari sun kai wa kwamitin fadar shugaban kasa hari a Legas

Ya ce wayoyinsa ba sa tafiya, duk a kashe, tun bayan kotu ta bayar da umarnin tafiya dashi gidan gyaran halin.

"Za a koma da Ndume kotu yau don cigaba da shari'ar. Tunda kotu ta bayar da zabi 3, kuma muna fatan zai cikase ko da zabi daya ne don su sake shi," kamar yadda majiyar tace.

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce wajibi ne jami'an tsaro su yi iyakar kokarinsu wurin tabbatar da sun dakatar da kashe-kashen da ya ta'azzara a Najeriya.

Shugaban kasan ya fadi hakan ne bayan samun labarin kisan Philip Shekwo, shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, jaridar The Cable ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng