Batan dabon Maina: Kotu ta bukaci a adana mata Sanata Ndume a gidan maza

Batan dabon Maina: Kotu ta bukaci a adana mata Sanata Ndume a gidan maza

- Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja, ta bayar da umarnin kama Sanata Ali Ndume

- Dama kotun ta umarci Sanata Ndume da ya gabatar da Maina gaban ta, kuma ya kasa

- A zaman kotu na ranar Litinin, alkalin kotun ya bayar da umarnin damke Ndume

Babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta bayar da umarnin damkar Sanata Ali Ndume, Sanatan jihar Borno, a kan batan Abdulrasheed Maina, wanda ya tsaya wa yayin karbar belinsa.

A zaman kotun na ranar Litinin, kotun ta umarci a kamo Ndume saboda rashin bayyana Maina wanda aka yanke wa hukunci a kan damfara.

KU KARANTA: Sanatan APC ya fusata da ministan ayyuka, ya alakanta kashe-kashe da miyagun tituna

Batan dabon Maina: Kotu ta bukaci a adana mata Sanata Ndume a gidan maza
Batan dabon Maina: Kotu ta bukaci a adana mata Sanata Ndume a gidan maza. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dan sanda ya bindige wani bawan Allah a otal, ya raunata wani na daban

Karin bayani na nan tafe...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel