Makashi ya fille wa mahaifi kai, ya halaka da har lahira a Kano

Makashi ya fille wa mahaifi kai, ya halaka da har lahira a Kano

- A ranar Litinin da daddare wani dan ta'adda ya je har gidan wani Malam Nuhu ya kashe shi a jihar Kano

- Bayan faruwar lamarin ne dan sa ya bi mutumin da gudu don ya kama sa, amma mutumin yayi ta sharba masa wuka har sai da shima ya mutu

- Al'amarin ya faru ne a kauyen Tumfafi da ke karamar hukumar Garko a jihar Kano, wanda yayi sanadiyyar mutuwar da da uba

A ranar Litinin, wani dan ta'adda ya kai wa wani Malam Nuhu mazaunin kauyen Tumfafi da ke karamar hukumar Garko da ke jihar Kano, hari, The Punch ta wallafa.

Kamar yadda masu gani da ido suka ce, dan ta'addan yayi yunkurin kashe Nuhu a gidansa kwanakin baya, har yana sharba masa wuka a hannu.

An ce mutumin ya tsere ne bayan ya kashe Malam Nuhu, bayan ganin hakan ne yasa dan Nuhu ya bi mutumin waje da gudu don ya kama shi.

Makashi ya fille wa mahaifi kai, ya halaka da har lahira a Kano
Makashi ya fille wa mahaifi kai, ya halaka da har lahira a Kano. Hoto daga thewhistle.ng
Asali: UGC

Sai dai mutumin ya mamayeshi, inda yayi ta datsarsa da wuka a jiki, har sai da ya kashe shi.

KU KARANTA: Batan dabon Maina: Kotu ta bukaci a adana mata Sanata Ndume a gidan maza

Ganau sun shaida yadda aka birne gawar Nuhu da ta dansa da misalin karfe 9 na safe, cikin matsanancin tashin hankali a kauyen Tumfafi.

Har yanzu ba a samu zantawa da jami'in hulda da jama'a ba na 'yan andan jihar ba, DSP Abdullahi Haruna, don an yi ta nemansa ta wayarsa amma abin ya ci tura.

KU KARANTA: Maina: Ndume ya kwana a gidan kurkuku, ya bayyana matakin da zai dauka

A wani labari na daban, tsohon ministan kudi, Olu Falae, ya yi korafi a kan sabon harin da makiyaya suka kai gonarsa da ke Akure, babban birnin jihar Ondo, Premium times ta wallafa haka.

Falae, wanda tsohon sakataren gwamnatin tarayya ne, ya ce makiyayan sun lalata kuma sun saci hatsi masu kimar miliyoyin nairori a gonarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel