Har yanzu fa bamu gama cire tallafin man fetur ba, Ministan mai, Sylva

Har yanzu fa bamu gama cire tallafin man fetur ba, Ministan mai, Sylva

- Ministan mai ya kwantar da hankalin yan Najeriya, yace har yanzu akwai tallafi

- Farashin man fetur ya tashi zuwa N170 ga lita a gidajen mai dake fadin tarayya

Duk da tsadar da mai ke yi, gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa har yanzu ba'a gama cire tallafi kan kayayyakin man fetur ba a kasar.

Haka Ministan Man fetur, Timipre Sylva, ya bayyana a hirar da yayi ranar Litinin da Seun Okinbaloye na Channels TV.

A cewar, wannan kawai somin tabi ne, yanzu aka fara cire tallafi kan kayan man fetur.

"Yanzu fa kawai muna kokarin tare abu ne kada ya balle. Bamu fara ainihin cire tallafin mai gaba daya ba ta bangaren kasuwar canji," Sylva yace.

"Idan muka cire tallafi gaba daya kuma muka bari mutane suna neman canji da kansu daga kasuwar canji kuma suna shigo da mai, farashin mai zai fi haka tashi."

"Gwamnatin tarayya ta san hakan zai yi tsanani kan mutane, shi yasa muke kula da lamarin."

Ministan ya ce tuni an cire tallafi daga kan Kalanzir da Gas, amma yana mamakin dalilin da yasa har yanzu aka gaza cire tallafi kan fetur.

Yayinda aka tambayeshi shin bai tunanin abin kunya ne a ce Najeriya za ta fara sayen mai daga Nijar, Ministan ya ce ba abin kunya bane.

"A ganina ba abin kunya bane," yace.

KU KARANTA: Buhari ya zabi Farfesa Mahmoud matsayin shugaban INEC, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan

Har yanzu fa bamu gama cire tallafin man fetur ba, Ministan mai, Sylva
Har yanzu fa bamu gama cire tallafin man fetur ba, Ministan mai, Sylva
Asali: Twitter

KU KARANTA: Daga karshe, Trump ya fara amincewa ya fadi zabe, ya amince a fara shirye-shiryen mika mulki

Mun kawo muku cewa gwamnatin Najeriya ta shiga sabuwar yarjejeniya da gwamnatin jamhurriyar Nijar na fara shigo da man fetur birnin Zinder.

The Nation ta ruwaito cewa Ministan arzikin man fetur na Najeriya, Temipre Sylva, da Ministan man jamhurriyar Nijar, Mr. Foumakoye Gado, ne suka rattafa hannu kan yarjejeniyar.

"Gwamnatin tarayyar Najeriya da Jamhurriyar Nijar ta rattafa hannu kan yarjejeniyar sufuri da ajiyar arzikin man fetur," ma'aikatar arzikin mai a Najeriya ta bayyana a wani jawabi.

Bayan tattaunawa da aka kasance anayi tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da shugaba Mahamdou Issoufou, na tsawon watanni hudu yanzu, kamfanin NNPC na Najeriya, da Societe Nigerienne De Petrole (SONIDEP), na Nijar sun amince da wannan harkalla.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel