Daga karshe, Trump ya fara amincewa ya fadi zabe, ya amince a fara shirye-shiryen mika mulki
- Ba tare da bata lokaci ba, Joe Biden ya fara nada wadanda zai yi aiki da su
- Ya alanta Antony Blinken matsayin Sakataren wajen Amurka
- Trump ya sauko daga tudun na ki, ya fara shirin sauka daga mulki a watan Junairu
Bayan makonni da kin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa, Donald Trump ya amince a fara shirye-shiryen mika mulki ga zababben shugaba Joe Biden, bayan jihar Michigan ta jaddada fadin shugaban kasar a zabe.
Dubi ga abubuwan dasuka faru ranar Litnin, Trump ya fara saduda bayan yakin da yake yi da sakamakon zaben ranar 3 ga Nuwamba, Aljazeera ta ruwaito.
Ma'aikatar harkokin gwamnati GSA, wata ma'aikata mai zaman kanta, ta tabbatar da cewa lallai Joe Biden ne ya lashe zabe kuma ta sanar da shi shirin fara shirye-shirye.
KU KARANTA: Sunayensu: Dangote ya shigar da karar wasu ma'aikatansa guda takwas
Shugabar GSA Emily Murphy, ta bayyana hakan ne bayan rashin nasara a yunkurin da Trump ke yi na kalubalantar sakamakon zabe a kotu.
Emily Murphy ta kasance mabiyar Trump kumata bata lokaci wajen amincewa da sakamakon.
A ranar Asabar, kotun jihar Michigan ta yi watsi da karar da Trump ya shigar.
"Ku sani cewa na yanke shawara na kaina, kuma bisa yadda doka da hujjoji suka tanada. Bantilastawa kowa ba - har da masu aiki a fadar White House ko GSA, " Emily ta bayyana a wasikar da ta aikewa Joe Biden.
Tabbatar da bayaninta, Trump wanda yaki amincewa da sakamakon zaben ya ce tuni ya umurci ma'aikatansa su fara shirye-shiryen mika mulki, amma ya lashi takobin ba zai daina yaki ba.
Trump ya bayyana a Tuwita cewa Emily Murphy "tayi abinda ya kamata kuma na umurci ma'aikatana su bi sahu."
KU KARANTA: Nuhu Bamalli Polytechnic: Injiniya Bello Atiku ya dawo gaban iyalinsa
A bangare guda, Jami'an jam'iyyar 'Republican' a jihar Wisconsin sun ce barayin yanar gizo sun sace Dala miliyan biyu ($2m) daga asusun da ake tara kudin yakin neman sake zaben Donald Trump a Amurka.
A ranar uku ga watan Nuwamba ne Amurkawa zasu kada kuri'unsu ga daya daga cikin 'yan takara biyu; Donald Trump, da Sanata Joe Biden, da ke neman kujerar shugaban kasa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng