Yanzu-yanzu: Buhari ya zabi Farfesa Mahmoud matsayin shugaban INEC, Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan
- Bayan makonni ana rade-radin, Buhari ya aike wasika majalisar dattawa
- Yanzu haka wa'adin farfesa Yakub ya kare matsayin shugaban hukumar INEC
- Yan jam'iyyar PDP a majalisa sun lashi takobin kin tabbatar da Yakubu zarcewa
Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi Farfesa Maumoud Yakubu domin zama shugaban hukumar zabe ta kasa watau INEC karo na biyu, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanto a zauren majalisa.
Shugaban kasan ya bukaci majalisar tayi gaggawar tabbatar da Farfesa Yakubu saboda ya kara shekaru 5 a INEC.
Buhari ya bayyana hakan ne a wasikar da ya aike majalisar, kuma shugaban majalisar Ahmad Lawan ya karantawa Sanatacoi ranar Talata, 24 ga Nuwamba, 2020.
DUBA NAN: An tsige kakakin majalisar dokokin Gombe, an nada sabo
KU KARANTA: Daga karshe, Trump ya fara amincewa ya fadi zabe, ya amince a fara shirye-shiryen mika mulki
A bangare guda, Sanatocin jam’iyyar adawa ta PDP a majalisar dattawa sun shirya domin hana a amince da sabon wa’adi ga Farfesa Mahmood Yakubu a hukumar INEC.
Jaridar This Day ta ce ‘yan adawan da ke majalisar tarayyar ba su goyon bayan Mahmood Yakubu ya sake shafe wasu shekaru biyar ya na rike da hukumar.
Hakan na zuwa ne bayan ‘yan majalisar tarayya sun dawo daga hutun da su ka je, yanzu an cigaba da sauraron zaman kare kasafin kudin shekarar badi.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng