PDP ta nada Saraki shugaban kwamitin sulhu na jam'iyya na ƙasa
- Babban jam'iyyar adawa PDP ta nada Sanata Bukola Saraki ya zama shugaban kwamitin sulhu na kasa
- Saraki zai jagoranci kwamiti ne da ya kunshi mambobi guda shida da aka zabo daga yankunan Najeriya
- Mambobin kwamitin sun hada da Sanata Pius Ayim, Liyel Imoke, Ibrahim Dankwambo, Ibrahim Shema da Mulikat Akande
Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta nada tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki a matsayin shugaban kwamitin sulhu na kasa mai mambobi guda shida.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Sanata Pius Ayim; tsaffin gwamnoni Liyel Imoke (Cross Rivers), Ibrahim Dankwambo (Gombe) da Ibrahim Shema (Katsina) da kuma tsohon shugaban marasa rinjaye na Majalisa, Mulikat Akande.
DUBA WANNAN: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya
Wannan sanarwar tana kunshe ne cikin wani sako da shafin Twitter na sakataren jam'iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ya wallafa a ranar Litinin.
Tunda farko, Kwamitin Gudanarwa na Jam'iyyar a ranar Litinin ya nada sabon kwamitin shugabannin jam'iyyar reshen Jihar Ebonyi kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Mataimakin jam'iyyar na kasa shiyyar Arewa, Sanata Suleiman Nazif ne ya jagoranci taron.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe masallata 5, sunyi awon gaba da liman da mutum 40 yayin sallar Juma'a a Zamfara
Wannan na zuwa ne bayan sakamakon ficewar gwamnan Jihar Ebonyi Dave Umahi daga jam'iyyar ta PDP inda ya sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki ta APC.
PDP ta yi ikirarin cewa Umahi yana kwadayin samun tikitin takarar shugabancin kasa ne shiyasa ya koma jam'iyyar ta APC sai dai a bangarensa ya musanta hakan.
Umahi ya ce rashin adalci da ake yi wa yankinsa ne yasa ya fice daga jam'iyyar ta PDP ya koma APC.
A wani labarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam'iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng