'Yan bindiga sun kashe masallata 5, sunyi awon gaba da liman da mutum 40 yayin sallar Juma'a a Zamfara
- 'Yan bindiga sun kai hari masallacin Juma'a a kauyen Dutsin Gari a Kanoma Jihar Zamfara
- 'Yan bindigan sun kashe mutane biyar bayan sun bude wuta wadda hakan yasa liman ya datse sallar
- Sun yi garkuwa da liman da wasu mutum 40 amma sun sako limanin da wasu cikin mutanen a ranar Asabar
'Yan bindiga a ranar Juma'a sun afka masallacin Juma'a a kauyen Dutsin Gari a Kanoma, Jihar Zamfara sun yi awon gaba da liman da masallata kimanin guda 40.
Kauyen da ya yi suna saboda noman rake yana fuskantar hare-haren 'yan bindiga a baya bayan nan.
DUBA WANNAN: An kama mutum biyu bisa zargin cin babbakakken naman 'yan sanda
Kwararran majiyoyi a kauyen sun shaidawa Daily Nigerian cewa maharan da suka taho a kan babura fiye da 100 sun kashe masallata 5 sannan suka raunta da dama.
Majiyoyin sun ce harbe-harben da 'yan bindigan da suka yi yayin da suka isa masallacin Juma'an ya janyo turereniya bayan liman ya yanke salla a raka'a na farko.
'Yan bindigan sun yi awon gaba da limanin mai suna Mallam Yahaya da kimanin mutane 40 a kan babura suka shiga daji da su.
Wani mazaunin kauyen, Sani Kanoma ya shaidawa majiyar Legit.ng an sako limamin da wasu daga cikin masallatan daga baya a ranar Asabar.
Mista Kanoma ya ce bisa dukkan alamu 'yan bindigan sun zo ne don sace manoman rake masu arziki sosai wadanda suka biya miliyoyin naira a matsayin kudin fansa.
Da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Zamfara, Mohammed Shehu ya ce zai bada cikaken bayani kan lamarin a ranar Lahadi.
A wani labarin, Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya siffanta Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin 'raɓa' a yayin da ya ke tsokaci a kan wani littafi da aka rubuta kan shugaban kasar mai taken "The Buhari in Us".
Yahaya Bello ya furta hakan ne cikin wani faifan bidiyo da ya bazu a shafunkan sada zumunta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng