Yanzu Yanzu: Tsohuwar kwamishinar lafiya ta jihar Bauchi Zuwaira Hassan ta rasu a hatsarin mota

Yanzu Yanzu: Tsohuwar kwamishinar lafiya ta jihar Bauchi Zuwaira Hassan ta rasu a hatsarin mota

- Allah ya yi wa tsohuwar kwamishinar lafiya ta jihar Bauchi, Dr. Zuwaira Hassan rasuwa

- Zuwaira ta rasu a hatsarin mota a safiyar yau Litinin, 23 ga watan Nuwamba, a hanyarta na dawowa Bauchi daga Plateau

- Marigayiyar ta rasu ta bar mijinta na sunnah da yara uku, za a yi jana'izarta da karfe 1:30 na rana

Shugabar sashin likitoci ta kwalejin likitanci, asibitin koyarwa na jamiar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi, Dr. Zuwaira Hassan ta mutu a hatsarin mota.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa hatsarin ya afku ne a safiyar yau Litinin, 23 ga watan Nuwamba a kauyen Zaranda, kimanin kilomita 36 daga garin Bauchi.

Dr. Zuwaira ta kasance kwamishinar lafiya a gwamnatin baya ta Mohammed Abubakar. Ta rasu tana da shekaru 46 a duniya.

Yanzu Yanzu: Tsohuwar kwamishinar lafiya ta jihar Bauchi Zuwaira Hassan ta rasu a hatsarin mota
Yanzu Yanzu: Tsohuwar kwamishinar lafiya ta jihar Bauchi Zuwaira Hassan ta rasu a hatsarin mota Hoto: Nairaland Forum
Asali: UGC

An tattaro cewa za a sallaci gawarta da misalin karfe 1:30 a babban masallacin asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa.

KU KARANTA KUMA: An damke madugun mai garkuwa da mutane da mai yi wa yan bindiga leken asiri a Katsina da Zamfara

Daga nan za a binne ta a makabartan Musulmai da ke a hanyar Gombe Road daidai da koyarwar addinin Islama.

Wani kanin marigayiyar, Garkuwa Adamu, jami’in hulda da jama’a na hukumar tsaro ta NSCDC reshen Bauchi, wanda ya tabbatar da lamarin a wayar tarho, ya bayyana cewa lamarin mutuwar ya sanyasu cikin dimuwa.

Ya ce: “Eh, da gaske ne, ta mutu a safiyar yau a wani hatsarin mota a kauyen Zaranda a hanyarta na dawowa Bauchi daga Jos, jihar Plateau.

“Su uku ne a cikin motar lokacin da lamarin ya afku. Abun bakin ciki ne sosai ka tashi da mutum yanzu sannan anjima ace babu shi, abun bakin ciki ne matuka.

“Tana da kwazon aiki sosai da jajircewa a kan aikinta. Za mu yi kewarta sosai.”

KU KARANTA KUMA: Dakarun soji sun kashe yan bindiga masu tarin yawa sun kwato makamai a Zamfara (hotuna)

Da aka tuntube shi, Shugaban hukumar hana afkuwar hatsarurruka, Yusuf Abdullahi, ya ce baida cikakken labari game da hatsarin tukuna.

Ta rasu ta bar mijinta da yara uku.

A wani labarin, al’umman kauyen Aljumma a jihar Zamfara sun bayyana cewa yan bindiga sun tarwatsa su bayan wani hari da suka kai masu a ranar Lahadi.

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa wani mazaunin kauyen ya sanar da ita cewa yan bindigar fiye da 50 sun kai farmaki kauyensu a kan babura sannan suka bude wuta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng