Da duminsa: An kubutar da manyan 'yan sanda tara da aka sace a Katsina-Zamfara

Da duminsa: An kubutar da manyan 'yan sanda tara da aka sace a Katsina-Zamfara

- A cikin makon nan ne aka samu labarin cewa 'yan bindiga sun sace wasu manyan jami'an 'yan sanda a tsakanin Katsina zuwa Asabar

- An samu labarin sace manyan jami'an ne ta hannun matar daya daga cikinsu bayan ya kira, ya bukaci a siyar da gidansa a biya kudin fansa

- Sai dai, a cikin wata sanarwa da rundunar 'yan sanda ta fitar ranar Juma'a, Frank Mba, ya ce an kubutar da dukkan jami'an

Rundunar 'yan sanda ta sanar da cewa an kubutar da manyan 'yan sanda tara, dukkansu ASP, da aka sace tun ranar takwas ga watan Nuwamba na wannan shekarar a tsakanin jihar Katsina da Zamfara.

An sace manyan 'yan sandan ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, Maidugurin jihar Borno.

A cikin wani jawabi da kakakin rundunar 'yan sanda, Frank Mba, ya fitar ranar Juma'a, ya ce wani binciken karkashin kasa da suka gudanar, bayan samun labarin sace jami'an, ya gano wurin da aka garkamesu.

KARANTA: Karin albashin Malamai: Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da kwamitin aiwatarwa

An sace jami'an a tsakanain garin Kankara zuwa Sheme a jihar Katsina sakamakon mummunan harin da wasu 'yan bindiga sanye da kayan soja suka kai a kan motar haya da suke ciki tare da wasu fararen hula.

Da duminsa: An kubutar da manyan 'yan sanda tara da aka sace a Katsina-Zamfara
Da duminsa: An kubutar da manyan 'yan sanda tara da aka sace a Katsina-Zamfara
Asali: UGC

"Rundunar 'yan sanda ta samu nasarar kubutar da manyan jami'anta guda tara da aka sace tun ranar 8 ga watan Nuwamba a tsakanin garin Kankara da Sheme a jihar Katsina yayin da suke tafiya a cikin motar haya da tsakar dare.

"Basa dauke da makamai, kuma basa sanye da kakin aikin dan sanda.

KARANTA: Kotu ta janye belin Abdulrasheed Maina, ta bada umarnin a kama shi

"Wasu 'yan ta'adda, dauke da manyan bindigu, da ake zargin 'yan bindiga ne, kuma sanye cikin kakin sojoji, su ne suka sacesu bayan sun kai wa motarsu farmaki yayin da suke tafiya cikin tsakar dare.

"Dukkaninsu masu mukamin ASP ne kuma suna kan hayarsu ta zuwa Gusau, jihar Zamfara, daga Maiduguri, jihar Borno a lokacin da tsautsayin ya faru," a cewarsa.

Mba ya ce biyu daga cikin jami'an yanzu haka suna asibiti ana duba lafiyarsu, yayin da sauran bakwai suna samun kulawa ta musamman.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, ƴan sanda a jihar Kano sun ƙwamushe wani saurayi mai shekaru 24 bisa zargin aikita laifin kisa da garkuwa da wata yariya ƴar shekara takwas, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel