An damke madugun mai garkuwa da mutane da mai yi wa yan bindiga leken asiri a Katsina da Zamfara

An damke madugun mai garkuwa da mutane da mai yi wa yan bindiga leken asiri a Katsina da Zamfara

- Hazikan sojojin Najeriya sun yi aikin kakkaba a jihohin Zamfara da Katsina da ke yankin arewa maso yamma

- A jihar Katsina, an kama wani madugun mai garkuwa da mutane da ake nema ruwa a jallo a karamar hukumar Kurfi

- Har ila yau a jihar Zamfara an kama wani Shafiu Suleman wanda ke yi wa yan bindiga leken asiri a yankin Kwatarkwashi

Hedkwatar tsaro ta bayyana cewa dakarun soji sun kama wani mai yi wa yan bindiga leken asiri da ake nema ruwa a jallo, Shafiu Suleman a kasuwar Kwatarkwashi.

Hakan na kushe ne a wata sanarwa da jagoran labarai a kan ayyukan tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya fitar a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba.

Ya bayyana cewa binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin shine makiri a sace-sacen wasu mutane da aka yi a yankin Kwatarkwashi da ke jihar Zamfara.

An damke madugun mai garkuwa da mutane da mai yi wa yan bindiga leken asiri a Katsina da Zamfara
An damke madugun mai garkuwa da mutane da mai yi wa yan bindiga leken asiri a Katsina da Zamfara Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yadda yan bindiga suka tarwatsa wani kauye a jihar Zamfara

Ya kuma ce bayan samun kiraye-kiraye masu cike da damuwa kan kasancewar yan bindiga a Gidan Ruwa, hanyar yankin Rukudawa da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, rundunar soji sun amsa kiran.

Enenche ya kuma bayyana cewa sojojin sun fatattaki yan bindiga yayinda suka tsere bayan hango su.

Sai dai an kashe wani dan bindiga, yayinda aka samo bindigar AK47 guda daya da mujalla dankare da harsasai 29. An kuma kama wasu yan bindiga biyu a cikin haka.

Hakazalika, bayan samun bayanan sirri, dakarun soji a ranar 22 ga watan Nuwamba, sun kama wani da ake zargin madugun mai garkuwa da mutane ne a karamar hukumar Kurfi da ke jihar Katsina.

KU KARANTA KUMA: Za mu farauto makasan Shugaban APC na Nasarawa, Gwamna Sule ya sha alwashi

A yanzu haka, wanda ake zargin wanda ya kasance a cikin jerin mutanen da ake nema ruwa a jallo yana nan a tsare kafin a dauki mataki na gaba.

A gefe guda, dakarun Operation Accord sun yi gagarumin nasara a mayar da hankali da suka yi wajen yaki da miyagu a yankin arewa maso gabas.

Dakarun sojin a ranar 21 ga watan Nuwamba, yayinda suke gudanar da aiki a kauyen Galadi da ke karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara, sun yi kicibis da yan bindiga.

A kan haka suka kashe yan bindiga biyu yayinda suka kwato bindigogin AK47.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel