Nigeria ta faɗa cikin matsin tattalin arziki mafi muni tun 1987

Nigeria ta faɗa cikin matsin tattalin arziki mafi muni tun 1987

- Alkallumar kiddigar abinda kasa ke samu sun nuna cewa Najeriya ta sake shiga matsin tatallin arziki a hukumance

- Matsin tattalin arzikin da kasar ta fada shine mafi muni da aka samu a kasar a shekaru 30 da suka shude

- Wannan shine karo na biyu da Najeriya ke fadawa matsin tattalin arziki a karkashin mulkin demokradiyya ta Shugaba Muhammadu Buhari

A hukumance, Najeriya ta fada cikin halin matsin tattalin arziki mafi muni cikin shekaru fiye da 30 kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

A cewar rahoton kiddidigar abinda kasar ke samarwa a shekara, GDP, ta Hukumar Kididdiga na Kasa, NBS, ta fitar a ranar Asabar, hada-hadar kasuwanci sun ragu da kashi 3.62 cikin 100 a watanni uku na karshen 2020.

Nigeria ta fada cikin matsin tattalin arziki mafi muni tun 1987
Nigeria ta fada cikin matsin tattalin arziki mafi muni tun 1987. Hoto daga @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Na gwammace a datse min kai a maimakon in bada haƙuri', martanin Bashir El Rufai ga masu sukar hotunansa da Nwakaego

Wannan shine karo na biyu da GDP din ke raguwa a jere tun matsin tattalin arzikin da kasar ta fada a shekarar 2016. Jumullan GDP din na watanni tara na farkon shekarar 2020 sun nuna alkallumar na -2.48%.

Lokaci na karshe da Najeriya ta samu irin wannan alkalluman GDP shine a shekarar 1987 a yayin da GDP din ya rage da kashe 10.8 cikin 100.

KU KARANTA: Gwamna Bala Muhammad ya ƙaryata rade-radin ficewarsa daga PDP

A cewar sakamakon da Bankin Duniya da NBS suka wallafa da majiyar Legit.ng ta yi nazari, wannan shine karo na biyu da Najeriya ke tsindimawa cikin matsin tattalin arziki a karkashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari - kuma na hudu a karkashin mulkinsa a shugaban kasa.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin Jihar Kogi za ta bullo da sabon haraji a kan kowanne gasashen burodi a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ma'aikatar kasuwanci da masana'antun tace harajin zai taimaka wajen kara samun kudaden shigar da ake samu na cikin gida.

Amma, kungiyar masu gasa burodi reshen jihar sun bayyana cewa basu goyon harajin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164