Yadda yan bindiga suka tarwatsa wani kauye a jihar Zamfara
- Mazauna kauyen Aljumma a jihar Zamfara sun shiga dimuwa bayan wani harin yan bindiga a ranar Lahadi
- An tattaro cewa maharan sama da guda 50 sun kai farmaki kauyen a saman babura inda suka fara harbe-harbe
- Jami’an tsaro sun yi nasarar dakile harin da fari amma kuma sai maharan suka sake dawowa lamarin da ya sanya mazauna yankin tarwatsewa don tsira
Al’umman kauyen Aljumma da ke karamar hukumar Maradun na jihar Zamfara sun bayyana cewa yan bindiga sun tarwatsa su bayan wani hari da suka kai masu a ranar Lahadi.
Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa wani mazaunin kauyen ya sanar da ita cewa yan bindigar fiye da 50 sun kai farmaki kauyensu a kan babura sannan suka bude wuta.
Amma kuma ya bayyana cewa jami’an tsaro da yan banga sun yi nasarar fatattakarsu amma sai suka sake dawowa daga bisani, lamarin da ya gigita mazauna kauyen har suka shiga daji don tsiratar da rayuwarsu.
KU KARANTA KUMA: Za mu farauto makasan Shugaban APC na Nasarawa, Gwamna Sule ya sha alwashi
Ya bayyana cewa: “mutanen gari na tserewa mata da kananan yara.”
Lamarin na zuwa ne bayan 'yan bindiga sun afka masallacin Juma'a a kauyen Dutsin Gari a Kanoma, Jihar Zamfara a ranar Juma'a, inda suka yi awon gaba da liman da masallata kimanin guda 40.
Kauyen da ya yi suna saboda noman rake yana fuskantar hare-haren 'yan bindiga a baya bayan nan.
Kwararran majiyoyi a kauyen sun shaidawa Daily Nigerian cewa maharan da suka taho a kan babura fiye da 100 sun kashe masallata 5 sannan suka raunta da dama.
Majiyoyin sun ce harbe-harben da 'yan bindigan da suka yi yayin da suka isa masallacin Juma'an ya janyo turereniya bayan liman ya yanke salla a raka'a na farko.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng