Mayakan ISWAP sun kashe sojojin Najeriya shida a Borno

Mayakan ISWAP sun kashe sojojin Najeriya shida a Borno

- Mayakan kungiyar ta'addanci ta ISWAP sun kai wa sojin Najeriya harin kautan-bauna a jihar Borno

- Sojoji shida da dan sa-kai daya ne suka rasa rayukansu a harin yayinda wasu da dama suka jikkata

- An kuma tattaro cewa mayakan sun yi awon gaba da wasu motocin dakarun sojin Najeriya guda biyu

Rahotanni sun kawo cewa sojoji akalla guda shida ne suka mutu sakamakon harin da mayakan ta’addanci na Islamic State West Africa Province (ISWAP) suka kai masu a ranar Asabar a jihar Borno.

An tattaro cewa lamarin ya afku ne a kauyen Burimari a yayinda tawagar sojojin ke a kan hanyarsu ta zuwa Baga, inda mayakan suka kai masu harin bazata.

Sashin Hausa na BBC ya ruwaito cewa wani kakakin rundunar sojan Najeriya, ya bayyana cewa suna bukatar lokacin domin sanin abinda ya kira da “gaskiyar al’amarin.”

Mayakan ISWAP sun kashe sojojin Najeriya shida a Borno
Mayakan ISWAP sun kashe sojojin Najeriya shida a Borno Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Sai dai kafar labaran ta ce wasu majiyoyi da dama ciki harda ta soji, ta sanar mata da cewa akalla sojoji shida ne suka rasa rayukansu tare da dan sa-kai daya, sannan fiye da 10 sun jikkata.

KU KARANTA KUMA: 2023: Dattawan arewa sun goyi bayan shugabancin Igbo

Har ila yau, rahotanni sun ce maharan sun kwace motar sojoji guda biyu.

Jaridar Vanguard kuma ta ruwaito cewa yawan sojin da suka mutu a harin kautan-baunar da mayakan suka kaiwa ayarinsu a Borno ya tashi zuwa takwas bayan an tsinci Karin gawawwaki biyu, kamar yadda wasu majiyoyin tsaro suka bayyana.

“Yawan wadanda suka mutu a harin ya koma takwas a yanzu. An gano Karin gawawwakin soji biyu,” in ji daya daga cikin majiyoyin.

“A yanzu ya koma soji takwas da dan bindiga daya aka kashe,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: Rahoto ya yi ikirarin cewa ana zawarcin Jonathan kan ya fito takara a APC

A gefe guda, Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya musanta labarin kai masa hari da 'yan ta'adda suka kara kai wa tawagarsa, jaridar Daily Trust ta wallafa.

"Ba a kai masa hari ba, balle tawagarsa," kamar yadda Malam Isa Gusau, hadimin Zulum na harkar watsa labarai ya sanar a wata takarda.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel