Tsintar gawar shugaban APC: Buhari ya yi martani tare da aike wa jami'an tsaro sako

Tsintar gawar shugaban APC: Buhari ya yi martani tare da aike wa jami'an tsaro sako

- Shugaba Buhari, ya ce wajibi ne jami'an tsaro su jajirce wurin samar da tsaro a Najeriya

- Ya fadi hakan ne bayan samun labarin kisan shugaban APC na jihar Nasarawa

- Ya ce za a yi bincike mai tsanani don gano wadanda suka kashe Philip Shekwo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce wajibi ne jami'an tsaro su yi iyakar kokarinsu wurin tabbatar da sun dakatar da kashe-kashen da ya ta'azzara a Najeriya.

Shugaban kasan ya fadi hakan ne bayan samun labarin kisan Philip Shekwo, shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, jaridar The Cable ta wallafa.

Sai da aka sace Shekwo a gidansa da ke Lafia, ranar Asabar da daddare, daga baya aka tsinci gawarsa.

A wata takarda ta ranar Lahadi, wacce Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya saki, ya yanki inda shugaban kasa yake fadin kokarin mamacin wurin bunkasa jam'iyyar, wanda ba za a taba mantawa da shi ba a tarihin APC din jihar Nasarawa.

Tsintar gawar shugaban APC: Buhari ya yi martani tare da aike wa jami'an tsaro sako
Tsintar gawar shugaban APC: Buhari ya yi martani tare da aike wa jami'an tsaro sako. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dogarin babban mutum a Najeriya ya harbe mutum 1 tare da yin mummunan rauni ga wani

Shugaba Buhari ya ce za a tabbatar an yi tsattsauran bincike don a gano ko aikowa aka yi don a kashe shi, ko kuma garkuwa da shi aka yi, tukunna aka kashe shi.

"Ina matukar jin takaicin kisan Philip Shekwo. Mutum ne mai kirki da fara'a.

"Ya yi matukar kokari wurin bunkasa jam'iyyar APC a jihar Nasarawa, ba za a taba mantawa da shi ba. Muna masa fatan rahama," cewar Buhari.

KU KARANTA: Zulum ya magantu a kan harin da ake rade-radin 'yan Boko Haram sun kai masa

A wani labari na daban, shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, Philip Tatari Shekwo, ya shiga hannun masu garkuwa da mutane.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Emmanuel Bola Longe, wanda ya tabbatar da hakan a wata hirar wayar tafi da gidanka da yayi da jaridar Leadership, ya ce 'yan bindiga masu tarin yawa ne suka tsinkayi gidan shugaban APC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng