Dogarin babban mutum a Najeriya ya harbe mutum 1 tare da yin mummunan rauni ga wani

Dogarin babban mutum a Najeriya ya harbe mutum 1 tare da yin mummunan rauni ga wani

- Wani dan sanda mai tsaron lafiyar wani babban mutum a Najeriya ya harbe wani tare da raunata wani

- Sannan a jihar Ekiti, wasu matasa masu zanga-zanga sun kashe wani dan sanda a hedkwatar 'yan sanda a ranar Juma'a

- Matasan sun afka ofishin 'yan sandan ne suna zanga-zanga a kan 'yan sanda sun boye gawar wani dan acaba, wanda wani direba ya kashe

Wani jami'in 'yan sanda mai suna Tishe Goji, ya harbi mutane 2, daya ya rasa ransa take a nan, daya kuma yana cikin matsanancin hali, jaridar Newswire ta wallafa hakan.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, al'amarin ya faru ne a wuraren Queen's Court a ranar Lahadi da safe, duk da dai har yanzu ba a gano sunan dan sandan ba,

A ranar Alhamis, wani dan sanda mai tsaron lafiyar kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya harbi wani mai sayar da jaridu a Abuja, inda ya mutu har lahira.

Dogarin babban mutum a Najeriya ya harbe mutum 1 tare da yin mummunan rauni ga wani
Dogarin babban mutum a Najeriya ya harbe mutum 1 tare da yin mummunan rauni ga wani. Hoto daga @vanguardngrnews
Asali: Twitter

Sannan an harbi wani dan sanda a wata zanga-zanga da matasa suka yi a wani ofishin 'yan sanda na jihar Ekiti a ranar Juma'a, kuma ya rasu take-yanke.

KU KARANTA: Na ga tsabar wulakanci yayin da nake aiki a fadar Buhari, Diyar Buba Galadima

Al'amarin ya faru ne bayan fusatattun matasa sun afka wa babban ofishin 'yan sanda da ke babban birnin jihar suna zanga-zanga akan yadda wani direba ya kashe wani dan acaba.

An kashe dan sandan ne lokacin da yake kokarin korar masu zanga-zangar.

Ran matasan ya baci ne bayan direban da ya kashe dan acaban ya bai wa iyayen mamacin N470,000, sannan 'yan sanda sun adana gawar.

Bayan hakan ne 'yan uwan mamacin suka afka ofishin 'yan sanda rai bace suna zanga-zanga, kamar yadda wani ganau ya tabbatar.

KU KARANTA: 2023: Ministocin Buhari 2 suna zawarcin kujerarsa

Bayan 'yan sandan sun lura zanga-zangar ta fara zama tashin hankali, sai suka fara jefa wa matasan barkonon tsohuwa suna harbi a sama, don su tsoratar.

Take a nan wani, cikin masu zanga-zangar ya harbi wani dan sanda a kafa, wanda sakamakon yadda jini yayi ta zuba ya rasa ransa.

Kakakin rundunar 'yan sandan, Sunday Abutu, ya tabbatar da mutuwar dan sandan amma ya ce matasan sun fara zanga-zangar ne bayan sun ji za a bai wa mai mashin din N150,000.

A wani labari na daban, an tsinci gawar shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, bayan an yi garkuwa da shi. Wata majiya da take kusa da iyalan mutumin ne ta sanar da jaridar PREMIUM TIMES a ranar Lahadi da rana.

Sannan wani shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, wanda bai so a ambaci sunansa ba, shi ma ya tabbatar da mutuwar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng