'Yan bindiga sun kutsa gidan dan majalisar tarayya, sun yi awon gaba da mutum 2

'Yan bindiga sun kutsa gidan dan majalisar tarayya, sun yi awon gaba da mutum 2

- Wasu 'yan bindiga sun kai hari gidan Abubakar Yahaya Kusada, wani dan majalisar wakilai daga jihar Katsina

- Kusada tsohon kakakin majalisar jihar Katsina ne, kuma yanzu yana wakiltar mazabar Kusada, Kankia da Ingawa

- Sun kwashe mutane 2 da suka taras a gidan, bayan sun nemi inda mahaifiyar dan siyasar take amma ba su same ta ba

Wasu 'yan bindiga sun kai hari gidan tsohon dan majalisar wakilai, Abubakar Yahaya Kusada, inda suka tafi da mutane 2, Daily Trust ta tabbatar.

Kusada tsohon kakakin majalisar jihar Katsina ne, kuma yanzu haka dan majalisar wakilai ne.

"Da misalin karfe 1 na dare, wasu 'yan ta'adda sun kai hari gidan Kusada, dan majalisa mai wakiltar mazabar Kusada, Kankia da Ingawa a jihar Katsina," kamar yadda majiyar ta tabbatar.

"Yan bindigan sun sace wasu hadiman gidansa guda 2, wata Talatu, da wani Suleiman," a cewar majiyar.

KU KARANTA: Muneerat Abdulsalam ta samu tallafi daga wata kungiya, za ta ga likitan kwakwalwa

'Yan bindiga sun kutsa gidan dan majalisar tarayya, sun yi awon gaba da mutum 2
'Yan bindiga sun kutsa gidan dan majalisar tarayya, sun yi awon gaba da mutum 2. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace shugaban APC a Nasarawa

"Sai da masu garkuwa da mutanen suka fara tambayar inda mahaifiyar dan siyasar take, aka ce musu ba ta nan, sannan su ka dauke mutane 2 da suka samu a gidan."

A wani labari na daban, wani jami'in 'yan sanda mai suna Tishe Goji, ya harbi mutane 2, daya ya rasa ransa take a nan, daya kuma yana cikin matsanancin hali, jaridar Newswire ta wallafa hakan.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, al'amarin ya faru ne a wuraren Queen's Court a ranar Lahadi da safe, duk da dai har yanzu ba a gano sunan dan sandan ba.

A ranar Alhamis, wani dan sanda mai tsaron lafiyar kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya harbi wani mai sayar da jaridu a Abuja, inda ya mutu har lahira.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng